Akwai Alamun PDP Ce Za Ta Lashe Zaben 2019, Cewar Jonathan

Goodluck Jonathan

Tsohon Shugaban Kasar Nijeriya Dakta Goodluck Ebele Jonathan ya ce, har yanzu jam’iyyar PDP na da karfi kuma za ta iya samun nasara a zaben shekarar 2019.

Jonathan, ya ce, duk da rashin nasarar da Jam’iyyar PDP ta yi a zaben 2015 ba zai karya lagon jam’iyyar ba, a yanzu matakan da  jam’iyyar ta ke bi alamu ne na samun nasara a babban zaben gaba na 2019.

Tsohon shugaban kasar, ya bayyana hakan ne, lokacin da tawagar jam’iyyar PDP ta kai masa ziyara a masaukinsa da ke Abuja.

Source: LEADERSHIP Hausa