Akwai alheri wajen shigo da kaya ta tashan ruwa – Tafida Mafindi

Alhaji Tafida Mafindi

Alhaji Isa Tafida Mafinda ya share shekara 30 yana aiki a hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa na Najeriya, wato NPA. A zantawarsa da Aminiya, ya yaba da sabon tsarin hana shigo da wasu manyan kaya ta kan iyakokin da ba na ruwa ba, inda ya bayyana dimbin alherin da ke cikin tsarin. Ga yadda hirar ta kasance:

Aminya: Za mu so ka gabatar da kanka?
Sunana Tafida Isa Mafindi yeriman Muri, bayan na gama karatu a kan sha’anin kudi da ake kira a Accountancy, sai na kama aiki a hukumar kula da tashoshin jiragen ruwan kasar nan. Na kai har matsayin babban jami’i a tsawon shekara 30 da na yi ina aiki a hukumar, kafin na yi ritaya.

Aminiya: Me za ka ce game da cece-kuce da a ke yi a kan dokar hana shigo da motoci ta kan iyakokin da ba na ruwa ba?

Kafa dokar mataki ne mai kyau saboda duk wata kasa da ta san abin da take yi tana amfani da tashoshin jiragen ruwanta ne wajen shigar da kaya, ko fitarwa da ke da nasaba da sauran kasashen duniya don taimakawa tattalin arzikinta da kuma samawa kasarta tsaro. Alfanun da ake samu ta wannan hanyan suna da yawa. A fuskar tattalin arziki kawai da farko duk wani jirgi da yazo yana da dillalinsa da a ke kira “Shipping Agent” wanda dan kasar ne da ke aiki a tashar  tare da ma’aikatansa ’yan Najeriya, za su karu, kuma gwamnati za ta karu da su. Sannan shi kansa jirgin zai biya kudin sauke kaya a tashar, mafi karanci shi ne Dala dubu 150 man’yan jirage irin masu dauko motoci kuma suna biyan har Dala dubu 250.

Sannan masu kayan za su biya hukumar kwastam kudin fito gwargwadon kima da kuma dokar da gwamnati ta sa a kan kayan, a wani kayan sai a biya masa haraji har na Naira miliyan 60 zuwa miliyan 100. Akwai kuma hukumar NIMASA da ke tare da masu dakon saukar da kaya ta hanyan amfani da na’ura, wani kayan sai an share kwana uku ko fiye ana aikin sauke shi, ’yan Najeriya ne suke yin aikin. Sannan ga wuraren ajiyi da ake kira terminal wanda wani kayan sai ya shekara a wajen ba a ida kwashewa ba, wurare ne da aka jinginar da su ga kamfanonin kasa da ke gudanar da su tare da ma’aikatansu. Masu manyan motocinmu irin tirela ko jiragen kasa na gwamnati su ne za su yi jigilar kayan da a kawo ta tashoshin nan da ke Legas, ko Fatakwal, ko Kalaba zuwa sauran sassan Najeriya

Aminiya: Akwai korafin cewa ana samun jinkiri wajen daukan kaya daga tashoshin nan idan aka kwatanta su da na jamhuriyar Benin ko kasar Togo?
Eh, tashar jiragen ruwa na jamhuriyar Benin da na Togo ’yan layuka ne kawai da jirgi zai kara ya sauke kaya savanin na Najeriya manya. Ba su da wajen ajiyan kaya, saboda haka idan jirgi ya tsaya, zai biya kudin fakin, da na fito, da na saukewa, mai kaya ya samu kayansa nan take saboda ba su da wajen ajiye kayan nan bare a masu binciken kwakwab da kuma tantancesu, ’yan kasar ne suke da wuraren ajiya in abin ajiyewa ne, mu ko a nan mu na da wuraren ajiya wato Terminal da ’yan kasa ke gudanarwa, amma a karkashin sa’idon jami’an tsaro na farin kaya, da na kwastam, da na NAFDAC da na NDLEA da dai sauransu saboda a kasar nan ne za a yi amfani da su, savanin na can da kashi 90 cikin dari duk za a shigo da su ne Najeriya mafi yawa ta varauniyar hanya.

Sai dai maganar gaskiya, kamar kowace kasa da Faransa ta rena, an fi samu karancin sata a wadancan tashoshin savanin na mu na nan da wasu da ke hulda da tashoshin ke sace wani abu daga jikin abin da aka kawo kamar fitilar mota, ko buhun suga, ko wani abu. Sai dai a yau muna da damar inganta lamarin a karkashin wannan gwamnatin, kuma wadda ke kula da hukumar wato Hajiya Hadiza, jaruma ce kamar mahaifinta wadda ya karantar da mu Dokta Bala Usman.

Aminiya: Wace matsala kake ganin za a iya fuskanta idan aka ci gaba da shigo da motocin nan ta wadannan hanyoyin?
Illolin su na da yawa. Na farko dai idan kasa tana wahala wajen magance matsalar tsaro ta hanyan kashe dimbin kudi da jami’an tsaro, babban mataki na farko da za a dauka na rage wahalar shi ne sa ido a kan kan iyakokin kasar, aiwatar da hakan ta kan dukkan iyakokin kasa kuwa mawuyacin abu ne. Wajibi ne sai an zavi wasu kevavvun wurare da za a girke na’urorin zamani da za su taimaka a kan hakan. Saboda wasu na iya fakewa da irin wadannan wurare su shigo da wasu miyagun abubuwa kamar kwayoyi, da makamai, da sauransu ta hanyan amfani da wadan nan abubuwan da aka ba su damar su shigo da su, ba tare da an iya hana su ba saboda yawansu.

Wasu kayan haka ake kawo su a cikin kwantena ba tare da an tantance kwantenar ba. A wancan kasashe saboda ba a can ne za a yi amfani da su ba, su dai burinsu su samu haraji a wuce da kayan. Sannan wadanda suka ci gajiyar sauke kayan gajiyarsa ’yan kasar ne, haka nan masu motoci, idan kuma aka zo kan iyakar Togo da Benin a biya haraji, idan aka zo na Nijar a biya, idan a ka zo na Najeriya sai wani gawurtaccen dan fito azzalumi da ya san almundahana da ma’aikata ya karvi aikin, ya biya ma’aikata, har ’yan fashi da ke kan hanyan duk ya sani ya biya su.

Sannan kuma a tsarin daukan kaya a tashoshinmu na Najeriya, tirela ba ta wuce daukan kwantena biyu wato kafa 20, to a Benin a kwai wata mota da a ke kira Giwa sai an ninka mata wannan, haka  za ta biyo hanya ba za a binciki kayan ba, ma fi yawa ba za a karvi haraji ga kuma illar kashe hanya saboda nauyin kaya. Sannan kuma wadanda ke kawo motocin nan daga Turai zuwa wadancan kasashen, kwarori ne da al’amuran ta’addanci ke dada kamari a kasashensu. Suna da wuraren ajiye matattun motoci a wadannan kasashe makota da ba su da dokar shekara, ko inganci, a tsarinsu, irin wadannan motoci kwandem a ke kiransu a Turai, dakon kawo su daga Turai ne kawai wahalarka duk farashin da ka sayar da su idan ka kawo riba ne, sai a bi da su ta wadannankasashe su amshi harajinsu mu kuma a shigo mana da su ta varauniyar hanya, savanin idan ta tashoshinmu ne ba za a bari ba saboda akwai dokan shekaran mota misali duk wadda ta shekara 10 da yinta, ba za a barka ka shigo da ita ba ko da nawa za ka biya. Shi ne kake jin suna cewa fanal bita, da bakaniki, da fakanaiza za su rasa aiki, saboda matsalar motoci ne ko kuma gudun tsiya da suke yi da su, to su bi ta kan titi mana su hutu ba da gyaran.

Akwai kuma wasu kanan haraji na VAT da za su taimakawa kasarmu, amma duk sai a rasa a sakamakon bi ta wadancan hanya. A saboda haka ina kira ga Shugaban kasa Nuhammadu Buhari da ya rufe kunnensa kawai a kan masu kirarye-kirayen a janye dokar.

Source: Aminiya