Akwai ‘yan Boko Haram a shugabannin Borno – Janar Iraboh

Kwamandan rundunar Zaman Lafiya Dole mai yaki da Boko Haram ya ce rundunar ta samu nasarar cafke wasu shugabannin al’umma a jihar Borno bisa zargin hannu a kungiyar ta Boko Haram.

Manjo Janar Lucky Iraboh ya ce kawo yanzu rundunar ta kama da dama daga cikin shugabannin da suka hada da wani shugaban wata karamar hukuma a jihar.

Mista Irabor ya kara da cewa wasu daga cikin shugabannin suna da alaka da kungiyar ta Boko Haram, a inda wasu kuma su ne ma suka kirkire ta.

Source: BBC Hausa