An ceto Jamusawan da aka yi garkuwa da su a Nigeria

‘Yan sanda a Nigeria

Bayanai da dumi-duminsu na ce wa an ceto turawan Jamus din nan guda biyu da aka yi garkuwa da su a yankin Kagarko da ke jihar Kaduna.

A ranar Laraba ne dai rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da yin garkuwa da Farfesa Peter Breunig da Johannes Buringer wadanda suka kwashe fiye da shekara goma suna nazari kan kayan tarihin al’ummar NOK da ke yankin.

Su dai mutanen biyu masu nazari ne kan tarihi na abubuwan da ke binne a karkashin kasa.

Sai dai kuma wasu jami’an gwamnati na cewa turawan sun yi kuskure wajen shiga dajin ba tare da neman tallafin jami’an tsaro ba.

Yanzu dai gwamnatin jihar Kaduna ta mika mutanen ga ofishin jakadancin kasar Jamus da ke Abuja, babban birnin Najeriya.

Source: BBC Hausa