An Yi Bikin Kaddamar Da Littafin Tarihin Giwar Sarkin Kano

A ranar lahadi 19\2\2017 aka yi bikin kaddamar da littafin tarihin rayuwar Uwargidan Mai Martaba Sarkin Kano Mallam Muhammadu Sanusi II, CON mai suna  (Giwar Sarkin Kano), Hajiya Fulani Sadiya Ado Bayero, wanda Sani Ali Kofar Mata ya rubuta.

Littafin dai ya kunshi tarihi da gwagwarmayar da Gimbiya Fulani Sadiya Bayero ta yi tun daga kuruciya har zuwa wannan lokaci.

Taron wanda ya shiga kundin tarihin masarautar Jihar Kano, an an gudanar da shi a babban dakin taro na Mumbayya, da ke Gidan Malam Aminu Kano.

Da farko an fara bude taron ne da addu’a da misalin kkrfe 11 na safe, sannan aka fara abin da aka taru dominsa. Inda Jakada, kuma masanin harsuna Afrika da Tarihi a Jami’ar Bayero da ke Kano, Farfesa Dandatti Abdulkadir ya yi jawabin maraba.

A jawabin nasa, Farfesa Dandatti ya yi kira ga jama’a cewa a su rika kokari wajen kiyayewa da muhimmancin lokaci a duk sa’ilin da aka gayyace su wurin taro, ya kuma yabawa ‘yan kwamitin gudanar da wannan aiki da kuma shi marubucin littafin.

“Yana kyau mu rika daukar lokaci da muhimmanci, domin ba ya jiran wani. Zan iya tunawa lokacin da muke tare da Mallam Aminu Kano. Wata rana za mu yi tafiya da shi, sai Gwamna Abubakar Rimi ya yi latti, duk da yana Gwamna, Mallam ya ce mu tafi kawai. Haka kuwa aka yi, dole sai daga baya Rimi ya biyo mu.

“Baya ga haka, ina jinjina ga wannan marubuci bisa namijin kokari da ya yi shi da ‘yan kwamitin shirya wannan taro.” In ji Farfesa.

Daga nan ne kuma Dakta Aisha Shehu ta sashen nazarin Tarihi a Jami’ar Bayero Kano ta yi sharhi game da littafin, da abin da ya kunsa. Ta kuma yabawa marubucin bisa kokari da ya yi wajen zakulo jarumar mace kamar Giwa har ya  rubuta littafi a kanta.

Sannan kuma ta yi jan hankali game da marubucin cewa kamata ya yi a ce ya bayyanawa duniya alakar Giwa a dawa da kuma ita Gimbiya Sadiya Ado Bayero, da har ta zama giwar sarkin Kano. Har ila yau, ta roki shi da idan za a sake buga littafin a lura da ka’idojin rubutu.

“An yi kokari wajen tsara littafin, sai dai akwai ‘yan kurakurai da ba a rasa ba, wadanda yana da kyau nan gaba idan za a sake buga littafin, a kiyaye su.” In ji ta.

A karshe ta yaba da salon da murubucin ya bi wajen samar da wannan babban kundi na tarihin rayuwar uwargidan Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammad Sanusi II CON.

Da yake nasa jawabin, Mai Martaba Sarkin Kano, wanda Wamban Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya wakilta, ya ce sun ji dadi matuka da aka samar da wannan littafi domin Gimbiya Sadiya Ado Bayero. Wadda ta kasance mace ce mai kokari da son taimakon al’ummarta. Saboda haka, ba su yi mamaki ba da suka ga har an kammala wannan littafi kuma cike da abubuwan nazari, duk da cewa ba shi ne littafin da aka fara rubutawa a kanta ba. Lallai suna farin ciki da haka kuma suna fatan marubuta za su ci gaba da zakulo irin wadannan mata don bayyana irin ci gaban da suke samarwa a kasa.

“Gimbiya Sadiya Ado Bayero ta kasance mace ce mai kokari da son taimakon al’ummarta. Saboda haka, ba mu yi mamaki ba da muka ga har an kammala wannan littafi kuma cike da abubuwan nazari, duk da cewa ba shi ne littafin da aka fara rubutawa a kanta ba. Lallai muna farin ciki da haka kuma muna fatan marubuta za su ci gaba da zakulo irin wadannan mata don bayyana irin ci gaban da suke samarwa a kasa.

Shugban Rukunin Kamfanoni Jifatu, Alhaji Sabitu Muhammad shi ne  ya jagoranci kaddamar da littafin akan kudi Naira Miliyan daya, inda ya sayi kwafe biyar. Daga nan kuma sai mataimakan masu kaddamarwa suma suka samu sanya albarkarsu kamar haka:

Gimbiya Sadiya Ado Bayero N200,000, Masarautar Katsina N200,000, Sarkin Karofin Kano N200,000, Ambasada Kabiru Mai Sabulu N10,0000, Alhaji Kabiru Dan Kullum N40,000, Dan Adalan Kano N100,000 da sauransu.

Taron ya samu halatar manyan mutane daga ciki da wajen Kano, da suka hada Sarkin Ringim, Hajiya Hadiza Ado Bayero, Alhaji Gambo Danpass (Dan Saran Kano) Alhaji Ado Ahmad Gidan Dabino MON, Editan Mujallar Muryar Arewa, Kabiru Assada da sauransu.

Source: BBC Hausa