Ba Zan Runtsa Ba, Har Sai An Fatattaki Handama Da Babakere

FARFESA YUSUF USMAN, shi ne Babban Sakataren Ma’aikatar Inshorar Lafiya Ta Kasa (NHIS), a tattaunawarsa da LEADERSHIPHAUSA, ya yi tsokaci kan irin badakalar da aka tafka a ma’aikatar tsawon shekaru, tun daga batun cin hanci, rashawa, handama, babakare. Har ila yau da matakan da ya dauka na kawo karshen matsalar, da kuma yadda ‘yan Nijeriya za su amfana da tsarin, da kuma sauran batutuwa. Ga Yadda ta kaya…

Ranka ya dade, wadanne ayyuka ne suka rataya a wuyan ma’aikatar NHIS?

To, manyan ayyukan da suke karkashin wannan ma’aikata tamu a bayyane suke, shi ne kula da harkokin lafiya da suka shafi dukkan ‘yan Nijeriya baki daya, ta hanyar bayar da rahotanni yadda abubuwa suke gudana ga manyan hukumomi. Har ila yau, suna ajiye kudade a wajenmu, idan rashin lafiya ta kama su, asibiti kawai za su a ba su magana, NHIS za ta biya masu.

Al’umma Nijeriya sun haura milyan 180, saboda haka sha’anin kula da ingancin lafiyarsu ya rataya a wuyansa NHIS. Kasancewar da yawan mutane ba sa iya samun damar ziyartar asibitoci yayin da suke fama da rashin lafiya, sai dai su zauna a gida.

Wannan na cikin ayyukanmu, na tabbatar da cewa dukkan marasa lafiya sun samu zuwa asibiti, ta hanyar wayar masu da kai da kuma sama masu saukakan hanyoyi kai kukansu ga likita.

Shin zuwa yanzu kun cimma kudurin da kuka dauka?

Hakikanin gaskiya zan iya cewa ba mu kai ga cimma kudurorin da muka sanya a gaba ba. Domin Nijeriya tana da mutane sama da milyan 180 ne, mu kuma a tsawon shekarun 12 da muka fara gudanar da wannan aiki ba mu kula da mutum milyan hudu ba, watau bai kai kaso daya bisa dari ba, yayin da sauran kasashe irin su Kenya, Rwanda, Ghana da sauran su, sun tasamma kaso 60 cikin 100. Batu na hakika ba mu cimma komai ba, har yanzu da sauran su tafiya, ba mu ma fara komai ba a takaice.

Ka yi magana kan nasarar da wasu kasashe suka samu, ko za ka yi mana karin haske?

Kwarai da gaske! Maganar da nake game da kasashen Ghana, Kenya, Rwanda da ire-irensu, sun samu nasara ba tare da wata matsala ba. Lokacin da muka zo, mun tafi har kasar Amurka muka kwaikwayon yadda suke nasu tsari don yi amfani da shi a Nijeriya, sai mutane suka fara kalubalantar shirin.

Magana ta gaskiya ita ce, sashen kula da harkokin lafiya yana cikin mummanan yanayi a Nijeriya, sam ba a shi muhimmanci da ya dace, musamman abin da ya shafi tallafin kudi.

Zan kara fadi, kamar yadda nake fada a koda yaushe, babu wani tallafi da bangaren lafiya yake samu daga wurin mahukunta. Tallafin Lafiya gaba yake da Tallafin Man Fetur, domin rashin kula marasa lafiya yadda ya kamata yana janyo asarar rayuka a wasu lokutan.

Duba da nasarorin wasu kasashe da ka lissafo, me kake ganin yake janyo irin wadannan matsaloli a Nijeriya,?

Babban dalili shi ne, ba mu samun cikakken goyon baya daga cikin gida. Akwai karancin kudaden gudanarwa da ake samu da wajen masu kawo tallafin. Ba a barin mu mu yi aiki yadda muke so, wasu na kokarin juya mu da tilasta mana yin abin da suke so. Haka zalika cin hanci da rashawa yana matukar tasiri a ma’aikatar.

Baya ga haka, akwai kalubale da ake fuskanta wajen biyan asibitoci kudaden da mutane suka bayar, a wasu lokutan sai wasu su kashe, maimakon yin amfani da su a inda ya ce. Kudin nan da ake tattarawa na wadanda suke ajiya ne, amma wani sai ya yi gabansa kansa da su. Ba a iya kula da marasa lafiya yadda ya kamata saboda ba su da isassun kudi a hannu. Ana kallo, an yi shiru. Na san maganar nan da nake yi barazana ce a garesu, amma ina son wayar da kan dukkan wadanda abun ya shafa su san hakikanin gaskiya.

Har ila yau, su kansu asibitocin da muke ba su kudin al’umma don kula da lafiyarsu, ba sa yin aiki yadda ya kamata. Suna tsanantawa kwarai wajen karbar kudi daga hannun marasa lafiyarmu. Duk wadannan na cikin manyan matsalolin da NHIS ke fuskanta.

 

Ka yi batun rashawa a NHIS, daga lokacin da ka dare kujerar jagoranci zuwa yau, wane hobbasa ka yi don magance matsalar?

Babbar magana! Lokacin da na zo, na ga abubuwa kala-kala na cin hanci da rashawa, zalunci, rashin kwarewa da rashin adalci. Mutane sun kasa rike amanar da aka dora masu, son zuciya, handama, babakere da rubda ciki ga kudaden ajiya. An yi sakaci matuka da har abubuwa suka lalace haka, mutane ba su samun ainahin abin da ya suka de bukata. Saboda wasu shafaffu da mai sun sanya komai a aljihunsu, sai abin da suke so za a yi.

Babu wani mutum da yake da iko kan harkokin gudanarwa NHIS, domin ta al’umma ce, su ne ke da hakkin yi hulda da wanda suka ga dama. Ko ni da nake matsayin Babban Sakatare, ba ni da ikon tilastawa mutum yin rajista da NHIS, kowa na iya canjawa kamar yadda ake canja Asusun Ajiyar Kudi ko kuma na kamfanonin fanso da inshora.

Saboda haka, aiki na farko da na fara yi shi ne tattaunawa da ma’aikata wadanda suke makusantana, manyan manajoji da matsakaita, har kananan ma’aikata ban bari, duk na yi magana da su. Na kawo tsarin kawar da cin da rashawa daga ma’aikatar, na fada masu cewa yanzu lokaci ne da za mu zo da sabbin abubuwa wadanda za su kawo ci gaba.

Ba na jin cikin ma’aikatun kasar nan akwai wadanda suka kai tamu kwararrun ma’aikata; muna da likitoci, injiniyoyi, lauyoyi, masana harkar lissafi da sauran fannoni, mutane dai masu ilmi. Irin wadannan kwararrun jagoranci kwarai kawai suke da bukata, shi ne kuma abin da nake kokarin samarwa yanzu.

Bayan na ji ta bakin ma’aikatana kan yadda abubuwa suke gudana, sai na ziyarci Shugaban Kungiyar Kwadago, Dakta Ayuba Wabba, saboda kudaden da muke sarrafawa yawanci na ma’aikata ne. Mun tattauna da shi sosai a matsayinsa na wanda yake jagorantar kungiyar da ma’aikata suka dogara da ita wajen kwato masu ‘yancinsu. Mun sake neman amincewa da yardarsu kan cewar lokaci ya yi da za a rike masu amana kamar yadda suke bukata. Har ila yau, na je wajen Shugaban Kungiyar PUC, Mista Boboye Kaigama, na fada masa irin sabbin shirye-shiryen da muke tafe da su game da tsarin ma’aikatar NHIS, kuma ya gamsu da maganganunmu matuka.

Yanzu kuma mun fara shirye-shiryen ganin Gwamnoni, Sarakuna, Shugabannin Ma’aikatu, Malaman Addinai, ‘Yan Kasuwa da sauran su, kasancewar suna shugabantar wani ba’adi na al’umma ne, mu kuma harkarmu ta jama’a ce, saboda haka suna da rawar takawa wajen wayar da kan mutanen da suke karkashinsu.

 

Akwai masu ganin NHIS tana bada magani wanda yake ba mai inganci ba, me za ka ce game da wannan?

Wannan ba gaskiya ba ne, magani sunansa magani, ba a canja masa suna. Na taba zuwa Kyamis a nan Abuja zan sayi magani, sai aka kawo min na wani kamfani aka ce min naira dubu biyar, sai na ce a kawo min wanda yake da farashi mai rahusa, sai aka kawo min na naira 200, na duba na ga duk aiki daya suke yi. Wannan shi muke bukata asibitoci su rika wayar da kan mutanenmu a kai. Masanin hada magunguna ne ni, babu wata rufa-rufa da za a yi min.

 

Akwai batun korafin da ake yin kan takaita bada magunguna, inda ake aka cire cutukan Kansa da Koda, me za ka ce kan haka?

Muna samun irin wadannan korafe-korafe kan ba a bada maganin cutar Kansa ko Koda, amma ba gaskiya ba ne. Hakikanin abin da yaka faruwa shi ne, muna kayyade magungunan da ake bayarwa ga wadannan cutuka. Misali a cutar Kansa, akwai matsayin da ake kaiwa kudin maganin ya wuce kima, a nan ne maganar kayyadewa za ta zo, domin wani aikin sai ya lakume milyoyin kudi. Likitan Kansa ne ni, na san komai game da ita.

Yana da kyau kowa ya sani, bangaren bada magungunanmu, muna magana ne kan abinda aka fi bukata na yau da kullum. Shi ne muke biya, amma wanda ya wuce tsarin da muke kai, majinyaci zai biyawa kansa. Wannan shi ne batu na gaskiya, tun da ba za mu kwashe kudin ajiyarmu baki daya don mutum guda ba.

Muna samun mutane da yawa musamman manyan likitoci da suke kawo gudunmawa. Wani zai ce shin zai bada kudi ne ga mutum daya, ko kuwa zai sanya kudin a inda milyoyin mata da yara za su amfana ta hanyar karbar magunguna? Da yawansu abokaina ne, ina ba su shawarar da ta dace, amma muna iya bakin kokarinmu wajen ganin ‘yan Nijeriya sun ci gajiyar wannan tsari na NHIS.

 

Tun lokacin da ka zo ake zargin ma’aikatarku ta debi mutane ba bisa ka’ida ba, me za ka ce game da wannan?

Mutane suna bukatar a wayar masu da kai; akwai bambacin tsakanin daukar sabon ma’aikaci wanda zai fara daga kasa, da kuma aro mutumin da tuni yake aiki a wani wuri, sai ka bukaci ya zo ya yi maka aiki a matsayin kwantiragi, wannan shi ne abin da na yi.

A dokar daukar ma’aikata ta kasa, a matsayina na Babban Sakatare ina da ikon daukar duk wanda na ga dama a mataki wanda yake na kwantiragi domin yin aiki na wucin gadi. Kuma za a rika biyansa ne daga wannan matakai.

Alhamdulillahi, duk mutanen da aka dauka, sun kasance masu bada gudunmawa ne ga ci gaban wannan ma’aikata ta fuskoki da dama, shi ya sa na zabe su, saboda muna fuskantar kalubale sosai daga bangaren hukumomin kula da ma’aikatu, hatta Kwamitin Majalisa Tarayya a wannan fannin bai kyale mu ba. Amma yanzu mun yi amfani da wannan dama mun dauki kwararrun ma’aikata a wurare da dama; shashen sadarwa, sashen yada labarai, sashen shari’a da sashen kudi; domin gudanar da ayyuka yadda suka kamata.

 

Amma akwai masu ganin a nuna wariya yayin karawa ma’aikata kwarin gwiwa musamman bangaren karin girma?

Shi ma wannan ba gaskiya ba ne, domin ko lokacin da muke wancan daukar, mun karawa mutane da yawa girma daga kasa zuwa sama. Tsarin daukar ma’aikatan wucin gadi bai hana mu karawa sama da mutum shida girma ba. Kuma dukkansu ma’aikata ne da na tarar da su a wurin. Duk wanda ya ce mun wari wasu, mun yi kara masu matsayi ya fadi son zuciyarsa ne. Shi karin matsayi ba da ka ake yi ba, ana duba cancanta ne, ita muka yi amfani da ita a wannan bangaren.

Ba ka ganin hakan bai gamsar da wasu kungiyoyi ba, musamman a mataki na kasa?

Shi ya sa tun dazu na fadi cewar na kai wa Shugaban Kungiyar Kwadago da Shugaban Kungiyar PUC ziyara, mun tattauna da su kan muhimman batutuwa.

Sai dai, akwai matsala da ake samu musamman da kananan kungiyoyi, wadda ba ta wuce ta zabar shugabanni ba. Ana samun tsaiko wajen fara hulda da su, sakamakon rikicin jagoranci. Wasu rikice-rikicen ma suna gaban alkali ba a kammala daidaitawa ba.

Amma kamar yadda kowa ya sani, babu ruwan NHIS game da rikicin kananan kungiyoyi, ba ma tsoma baki a ciki, saboda magana na gaban kotu. Abin da kullum nake fada shi ne, idan har ana son magance wannan rikici dole a yi gaskiya da adalci ba tare da duban daga ina mutum ya fito ba.

Abin da ban yarda da shi ba, wani ya yi amfani da mu don biyan bukatar kansa. Aiki na zo yi, kuma shi zan mayar da hankali a kai.

Wane tsokaci za ka yi kan masu fadin ana fifita al’ummar wani yanki?

Wannan ma ba gaskiya ba ne, zance ne maras tushe ballanatana makama. Domin kwanan na muka dauko mace daga EFCC take jagorantar sashen yaki da rashawa, a karon farko daga Jihar Kebbi. Har ila yau, sashan sadarwarmu ya kai matsayin yin gogayya da takwarorinsa na duniya, shi kuma dan jihar Zamfara ke kula da shi. Babban Manajan kula da ma’aikata kuma daga Taraba ya ke; haka dai kowane mukami aka tsara. Idan na ji mutane suna maganar bangarenci sai in rike kaina, ina matukar mamaki.

Ni bukatata a yi aiki yadda ya kamata bisa tsari, matsalolin da NHIS ta ke ciki, a kawo karshensu. Babu wanda zai zo nan yana maganar bangarenci bayan mutane suna kokarin ganin sun samu abin da suke so daga garemu. Kamata ya yi a kula sosai da mutane da suke zuwa: Me ya kawo su? Me suka zo yi? Mene ne dalilinsu? Mun zo don mu yi aiki ne, kuma za mu yi da yardar Allah, babu wanda zai dauke hankalinmu da batun bangarenci.

Sai dai abin da zan yi magana a kai nan shi ne, duk yadda ka kai da kokarinka, ba za ka gamsar da kowa ba. Dole sai wasu sun yi korafi. Doka ta bawa kungiyoyi dama su yi abin da suke ganin shi ne daidai babu wanda zai hana su. Kawai dai ba za a bar su su wuce gona da iri ba, musamman wajen yin rubda ciki ga kayan Gwamnati ko kuma cin mutunci wani.

Wasu da dama sun dauka sai ma’aikatan gwamnati masu daukar albashi ne kadai za su iya amfana da wannan shiri. Ya za a yi wanda ba ya aikin gwamnati ya amfana?

Wannan shiri namu na NHIS shiri ne da aka bullo da shi don amfanar duk wani dan Nijeriya. Saboda haka ba sai lallai sai ma’aikacin gwamnati ne kadai zai amfana ba. Misali, akwai wani tsari da muke da shi wanda a ke ce ma ‘Boluntary Contribution Scheme.’ A wannan tsarin, misali za a iya samun wani dan siyasa, ko mai hali ya zabi wani asibiti ya ware wasu kudade masu yawa, ya je asibitin ya yi masu rajista da wannan shirin, inda zai biya ma’aikatarmu N15,000 kan kowane mutum a shekara daya.

Misali a ce a wannan shekara ta 2017, idan aka biya wa mutum wannan N15,000, to duk lokacin da ya ji wata rashin lafiya zai garzaya wannan asibitin da aka yi masa rajista ya ga Likita, kuma a ba shi magani bisa rangwame, inda zai biya kashi 10 cikin 100 kacal na duk kudaden da aka caje shi a asibitin.

Sannan kuma akwai tsarin da muke da shi na ‘Community Contribution Scheme.’ Shi kuma wannan, wani tsari ne da muka kafa domin al’ummar Unguwa, ko Gari, inda za su hada kungiya su tattara kudadensu su shiga wannan tsari da na ambata a baya. Tsari ne mai kyau, wanda jama’a za su amfana da shi matuka.

Saboda haka wannan shiri na NHIS, shiri ne da gwamnatin tarayya ta bullo da shi domin taimaka wa marasa galihu su samu ingantacciyar kiwon lafiya, ba wai sai ma’aikacin gwamnati ba. Shi ma’aikacin gwamnati, ma’aikatarsa ce ke bisa masa wadannan kudaden, bambancin ke nan.

Mene ne fatanka game da NHIS?

Fatana bai wuce kawo karshe rashawa da cin hanci a NHIS ba, da kuma tabbatar da cewar ana gudanar da komai bisa doka da oda, kwarewa da cancanta. Shi ne abin da muke ta kokari a kai. Samar da ma’aikata kwararru, wadanda za su bullo mana da hanyoyin ci gaba.

Baya ga wannan, muna so mutane su kara amince wa da mu, su gamsu cewar duk abin da muke yi saboda su ne. Ta yadda za mu yi hakan kuwa shi ne, mu tashi daga Birnin Abuja mu shiga lungu da sako na kasar nan, mu wayar da kan al’umma don a samu kari mutane. Na fada cikin milyan 180 da ke kasar nan kwata-kwata mutun milyan hudu muka samu damar hulda da su, yayin da wasu kasashe tuni sun yi nisa.

Zan yi kokari wajen bullo da sabbin hanyoyi da za su ba mu damar kara fadada tasoshinmu; tun daga farko Sahara har zuwa yanki Neja-Delta. So nake kafin lokacinmu ya yi mutane su fahimci irin aikin da muka yi na samar da karin jama’a a wannan tafiya.

Ina da burin ganin harkar lafiya tana samun cikakkiyar kulawa da tagomashi a kasar nan, shi ya sa na samar da sashen bin diddigin yadda lamurra suke tafiya. Da ma muna biyan asibitoci ne duk bayan wata uku, amma da na zo muna biyan su duk wata saboda su gudanar da aiki yadda ya kamata. Marasa lafiyar da suke karkashinmu sun fuskanci matsala sosai, shi ya sa muke ajiye jami’ai a wasu asibitoci domin su kula da yadda ake kula da marasa lafiyar da suke karkashin kulawarmu. Wannan shi ne abin da muke yi, kuma za mu ci gaba da ya yi cikin yardar Allah.

Source: LEADERSHIP Hausa