Bamu Da Sha’awa a Rikicin Jam’iyyar PDP, Inji APC

Taron PDP bangaren Sanata Ahmadu Makarfi

Jam’iyyar APC tace bata da wata sha’awa a rikicin jam’iyyar adawa wato PDP, wanda ma hakan ne yasa taki cewa komai akan zarge zargen da jam’iyyar ta PDP take yi mata saboda girmama hukuncin bangaren shari’a.

A jawabin da publicity secretary ya sanya wa hannu, Bolaji Abdullahi ya musanta duk wani zargi da bangaren Sanata Makarfi yake yiwa jam’iyyar ta APC da cewar ita ce ta sanya ‘yan sanda suka hana mambobin na PDP daga aiwatar da taro a babban dakin taro na ICC dake Abuja.