Barcelona ta kafa tarihin da ba a taba yi ba

Barcelona

Barcelona ta kafa tarihi a gasar Zakarun Turai ta Champions League bayan da ta zamo kulob din farko da ya cancanci zuwa wasan dab da kusa da na karshe duk da rashin nasarar da ya samu a zangon farko na ajin kungiyoyi 16.

A zangon na farko na wasan dai kulob din Paris St-Germain ya ci Barcelona 4-0, a gidansa.

A ranar 14 ga watan Fabrairu ne dai kungiyoyin biyu suka taka ledar.

To amma a zango na biyu na wasan da suka yi da yammacin Laraba a Nou Camp, Barcelona ta kori PSG din daga kasar bayan da ta ci ta 6-1.

Dan wasan kulob din, Luis Suarez ne dai ya fara cin kwallon a minti uku da fara wasan sannan kuma kwallo ta biyu ta samu ne bayan da dan wasan PSG, Layvin Kurzawa ya ci gidansa.

Lionel Messi ne kuma ya ci wa Barcelona kwallo ta uku a bugun fanareti sannan Neymar ya zura ta hudun, a inda kuma Suarez ya kara daga ragar PSG a karo na biyu.

Sergi Roberto ne ya ci kwallo ta shida wadda kuma ita ce kwallonsa ta farko a wannan kakar wasannin.

Wannan ne kuma ya kawo kungiyoyin biyu samun jumullar kwallaye 6-5, a zangon wasannin biyu na ajin kungiyoyi 16 da suka yi a gidan juna.

Yanzu haka wannan shi ne karo na goma da Barcelona ke zuwa wasan dab da kusa da karshe a gasar ta Champions League.

Yadda Barca ta kafa tarihi cikin mintuna da kuma jumullar kwallaye:

 • 3: Luis Suarez , Barcelona 1-0 PSG (1-4)
 • 40′: Layvin Kurzawa ya ci gidansa, Barcelona 2-0 PSG (2-4)
 • 50′: Lionel Messi ya ci a dukan fanareti, Barcelona 3-0 PSG (3-4)
 • 62′: Edinson Cavani , Barcelona 3-1 PSG (3-5)
 • 88′: Neymar ya ci daga bugun tazara, Barcelona 4-1 PSG (4-5)
 • 90’+1: Neymar ya ci a dukan fanareti, Barcelona 5-1 PSG (5-5)
 • 90’+5: Sergi Roberto , Barcelona 6-1 PSG (6-5)

Tarihin da Barca ta kafa a Nou Camp ya wuce irin na wadannan:

 • Deportivo v AC Millan (2004 Gasar Champions League)
 • Borussia Monchengladbach v Real Madrid (1985-86 kofin Uefa)
 • Leixoes v La Chaux-de-Fonds (1961-61 a gasar Cup Winners’ Cup)
 • Partizan v QPR (1984-85 gasar Uefa)

Me manajojin kungiyoyin ke fadi?

Manajan Barcelona: Luis Enrique:

“Hakika dare ne mai wuyar gaske wanda ba za a iya kwatanta shi da fatar baki ba.”

“Wani abu ne mai kama da fim din abun tsoro, ba ma wasan kwaikwayo ba, ya wakana a filin wasa na Nou Camp.”

“Jajircewar da ‘yan wasana suka nuna ne ya sa aka samu wannan nasara.”

Manajan Paris St-Germain: Unai Emery:

“Gaskiyar magana mun zubar da damarmu kuma mun fahimci haka.”

” Wasa ya subuce mana a minti biyun karshe bayan mun samo bakin zaren tun kafin zuwa hutun rabin lokaci. Ba karamin aikin Barcelona ne ba idan kuka hadu da su a gidansu.”

“A karshen wasan, sun yi mana wasa kuma a nan ne suka kasa mu.

Source: BBC Hausa