Bikin Auren Zawarawan Kano Ya Ci Karo Da Tasgaro

  • ‘Dokar Aure Ba Gudu Ba Ja Da Baya’

Ranar Lahadin da ta gabata ne Gwamnatin Kano ta yi bikin daura auren zawarawa 1,520 bayan gamuwa da tasgaro nan da can da ya hana gudanar bikin a baya.

Bikin an gudanar ne a Masallatan Juma’a na Sarki, na Murtala da kuma na Khalifa Sheikh Muhammad Rabiu da ke Goron Dutse, sannan kuma aka shaida sauran dauren auren zawarawan a kanannan hukumomin Jihar Kano 44, inda a kowacce karamar hukuma aka daura auren zawarawa 15.

Tun da farar safiyar ranar Lahadin ne aka yi ta ganin angwaye cikin anko, kowa na tunkarar inda aka tsara daura auren nasa, sannan kuma dukkan wuraren daurin auren Jami’an Hisba sun killace domin tabbatar da komai ya gudana cikin kwanciyar hankali.

Bayan gudanar da daurin auren zawarawa 1,520, sai aka hallara a babban dakin taro na ‘Coronation’ da ke fadar Gwamnatin Kano. Malamai sun yi nasiha ga angwaye da amare domin samun dorewar auren.

Da yake gabatar da jawabinsa a wurin taron, Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ce duk wani aikin alhairi yana bukatar lokaci matukar ba awon igiya ba ne, “hakan tasa muka baiwa hukumar Hisba isasshen lokaci domin tantance abubuwan yadda ya kamata”.

Ya kuma yi tsokaci kan masu lalurar cutar kanjamau musamman yadda aka samu shawarwarin likitoci kan wannan matsala. Gwamna Ganduje ya yi addu’ar samun karin dankon soyayya tsakanin ma’auta, ya kara da cewa “batun auren zawarawa ba lamarin siyasa ba ne hidima ce ta al’ummar Kano. Duk wanda ke zaune a Jihar Kano na da damar shiga wannan shiri ba mu ce a cire sunan kowa ba, Addinin Musulunci ba shida wani banbancin kabila kuma kowacce jam’iyya kake muna cewa da Kai ‘Jabbama’, ka zo mu daura maka aure namu ne kai a koda yaushe”.

A nashi bangaren, mai martaba Sarkin Kano, Malam Muhammad Sunusi, ya ce dokar da yake son bujuro da ita kan aure a jihar ba gudu babu ja da baya.

Sarkin wanda ya tabbatar da hakan yayin jawabi a lokacin auren zawarawa 1520 da gwamnatin jihar Kanon ta gudanar, ranar Lahadi, ya ce, dokokin auren ne kawai za su taimaka wajen kawo karshen matsalolin da suka dabaibaye al’umma.

Sarki Sunusi ya kawo wani misali dangane da yadda marasa karfi kan yi aure su kuma hayayyafa ba tare da kula da yaran nasu ba.

“Wata mace ta kawo min karar mijinta cewa ya sake ta alhali suna da yara 10 tare, saboda haka tana son a ja hankalin mijin nata wajen daukar nauyin yara guda bakwai, a inda ita kuma za ta kula da sauran ukun.”

“Sai na kirawo mijin na fada masa korafin tsohuwar matar tasa, a inda ya ce min ai yana da wata matar kuma suna da ‘ya’ya takwas, ka ga ke nan yana da yara 18 shi kadai.”

Sarki kara da cewa ya tambayi sana’ar mutumin, a inda ya ce masa “sana’ata shushaina”.

Wannan ne in ji Sarki Sunusi ya sa shi lasar takobin ganin an yi dokar da za ta taka wa irin wadannan halayyar burki.

Sai dai kuma sarkin ya nemi masu hannu da shuni masu mata daya da su kara, sai dai kuma Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ce idan dai har mutum yana samun abin da yake so daga wurin matarsa, to babu dalilin karawa duk da yana da halin yin hakan.

Shugaban Kwamitin gudanarwar hukumar Hisba ta Jihar Kano, Sheikh Ibrahim Shehu Mai Hula wanda ya fara gabatar da jawabin maraba ya yi godiya bisa wannan babban aikin alhairi da Gwamna Ganduje ya aiwatar, ya tabbatar da cewar akwai bukatar tabbatar gaskiya a tsakanin miji da mata.

Haka Kuma shehun Malamin ya tabbatar da cewar ba wanda zai kawowa al’ummar Kano wata dokar hana karin aure, “Gwamna da kuma shugaban majalisar dokokin Jihar Kano, mun tabbatar ba za su amince da duk wani kudurin kafa dokar hana karin aure a Jihar Kano ba”.

Babban Kwamanda Hisba na Jihar Kano wanda aka gudanar da wannan daurin aure karkashin kulawar hukumar da yake jagoranta, ya bayyana cewar sai da aka gudanar da gwajin lafiyar ma’auratan kafin amincewa da daurin auren kowannen su. Haka kuma ya ce sharuddan da aka gindaya ga duk mai bukatar shiga cikin wannan shiri su ne: tabbatar da ingacin lafiya, shaidar mai unguwa da kuma makwabcin ango sai kuma tabbacin sana’a.

Kwamandan Hisbar ya tabbatar da cewar Gwamna ya yanke hukunci kan dokar da ake kokarin samarwa kan karin aure a Kano, inda yace Gwamna ya tabbatar  da cewa bayan gama tsara dokar sai an gabatarwa da malamai wannan doka sun duba ta,  idan akwai wani abu da ya ci karo da shari’a su nuna rashin dacewarsa.

LEADERSHIP Hausa ta samu halartar wasu kananan hukumomin domin ganin yadda daurin auren ya gudana.

Shugaban  Karamar Hukumar Gaya, Alhaji Abba Muhammad Gamoji ya bayyana wa wakilinmu cewar ko shakka babu duk wanda ya kalli fusakun angwayen nan da amare ya san suna cikin farin ciki marar adadi. Ya ce Gwamnatin Kano karkashin Dakta Abdullahi Umar Ganduje ta samar da kudaden da aka sayawa daukacin wadanda aka daurawa wannan aure kayan daki irin na kowacce amarya ‘yar gata, sannan kuma an biya wa kowace amarya sadakin naira 20,000 tare da saya wa angwaye shaddar anko baki dayan su”.

Tun lokacin shigowar wannan Gwamnati ne aka shelanta yiwa zawarawa auren amma bai yiwu ba sai a wannan karon, kan haka wasu ke ganin gwamnatin jihar ta yada kwallon mangwaro don ta huta da kuad musamman bisa yadda wasu daga cikin zawarawan suka rika shiga kafafen yada labarai suna kokawa kan rashin daurin auren a kan kari.

Source: Leadership Hausa