Binciken masana ya gano fa’idar cin tsire da kayan lambu

An dai shafe shekaru aru-aru a duniya ana gudanar da sana'ar sayar da nama, da tsire ko kuma balangu har ma da gasasshiyar kaza.

Masanan sun ce cin tsire da kayan lambun na rage hadarin kamuwa da cutar Kansa

Jama’a na cin nau’in gashin ne dan jin dadi ko samun dandano a baki, musamman ma dai idan ka na da kudi a lalitarka.

To amma yanzu, lamarin ya sauya salo mai ban mamaki wanda kwararru a bangaren kiwon lafiya suka shigo cikin batun gadan-gadan.

Tunanin ku su ma sun fara sana’ar ta saida tsire da balangun?

Wani bincike da wasu masana suka gabatar sun gano cewar, cin gasasshen nama kamar tsire da balangu da kayan lambu da tumatir da albasa na rage hadarin kamuwa da cutar daji ko cancer.

To sai dai ba kowane mai sayar da naman ba ne ke amfani da albasa ko kuma kayan lambun wajen sayar da naman.

Tun kafin bayyanar wannan bincike dai, masu wannan sana’a suka fito da salon yanka kabeji, da gurji da tumatur da albasa, da koren tattasai mara yaji a wasu lukutan ma har da tafasasshen karas dan daukar hankalin abokan huldarsu.

To ko yanzu da bincike ya tabbatar da hakan,masu sayar da nama za su bunkasa amfani da irin wadannan kayayaki ?

Fatan masana game da wannan bincike shi ne, masu sayar da nama da masu saye su fahimci amfani da ire-iren wadannan kayayaki a lokacin da za su amfani da gasashen nama, tsire ko balango ,domin kasancewa cikin koshin lafiya.

Source: BBC Hausa