Bindigogi 661: Wa Yake Son Bala’i Ga Nijeriya?

A duk lokacin da irin wannan abu ya tarar da kai a rayuwarka, zaka nemi tsari daga Allah akan mugun ji da mugun gani, ka tara yawun bakinka waje guda ka tsirtar, sannan ka sake tambayar kanka shin haka lamari yake ne ko kuwa?

A wannan watan ne manyan alamu suka nuna cewa akwai wani mummunan shiri da wasu suke wa kasar nan, amma abin tsoron ma shine yadda ba a san ko su waye ba! Kana kuma me suke nufi da Nijeriya?

To amma abun tashin hankali da ya faru kwanan nan ya ishi ya hana duk mai tunani barci, ya isa ya saka jami’an tsaronmu cikin damuwa, ya isa ya saka ‘yan kasuwanmu cikin zulumi, ya isa ya saka shugabanninmu cikin damuwa, sannan kuma ya farantawa munafukai rai.

Kafafen yada labarai sun ruwaito batun kame sabbin bindigogi har guda 66, wadanda aka shigo da su daga Kasar Chana. Ba fa bindigogi uku ko hudu ba! Har guda 661 aka kama. Wannan babban labari ne a wurin ‘yan jarida, babban abun tashin hankali ne ga duk wanda ya san me ake kira bindiga kuma ya san illarsu musamman a hannun mugun mutum.

Babban abin tambayar da ya kamata mu tambayi kanmu shine, su wanene suka yi odar makaman sannan kuma me zasu yi da su? Su wa za a aiwatar da makaman akan su sannan akan wane dalilin? Sannan wa ya sayar musu da muggan makaman, me yasa ya yarda zai sayar musu?

Wannan labarin fa yana zuwa ne kwanaki kadan bayan an kama wasu jirage masu saukar ungulu da aka shigo da su ba bisa ka’ida ba. Babu wanda yasan me za a yi da jiragen da aka shigo da su kasar nan a sace.

Wannan babban ishara ce dake nuna mana halin da Nijeriya ke ciki, a daidai lokacin da ‘yan ta’addan Neja-Delta ke fasa bututun mai da muggan makamai a yankin Kudu. Sannan wasu dake shigar makiyaya na nan suna kashe mutane da muggan makamai a yankunan Arewa, ciki har da Kaduna wanda ke fama da danyen rikicin a yanzu.

Haka ma Arewa maso Gabashin kasar nan, inda muke fama da tashin boma-bomai da kuma kai kananan hare-hare kan al’umma daga ‘yan ta’addar Boko Haram. Haka kuma a cikin watan Janairun nan aka samu wani Fasto mai suna Johnson Suleiman ya nemi mabiya majami’ar shi da su kashe Fulani a duk inda suka gansu su kawo masa kawunan.

Haka zalika Gwamnan Jihar Taraba, Darius Ishaku ma ya gabatar da irin wannan kira ga jama’arsa, inda ya ce su tashi su kare kan su! Daga baya kuma ya lashe maganganun nasa. Duk a cikin watan Janairun nan.

To, ga wanda yake da tunani, ya san cewa wadannan abubuwa suna da alaka da makaman da ake shigowa da su. Don haka a kasar dake cikin wannan rudani, idan aka kama makamai masu yawa irin wadannan, an ya kuwa ba abu ne da zai nuna mana cewa lallai kasar na cikin halin ni ‘yasu.

Makon da ya wuce wata jarida ta ruwaito cewa mutumin da aka kama da makamai a Jihar Adamawa. Inda ya bayyana cewa, shaidun da lauya mai kare wanda ake tuhuma ya gabatar duk sun ce “wanda ake tuhumar ya mallaki wadannan makamai ne a lokacin da wasu jami’an tsaro suka yi musu gargadi da su fito da makamansu saboda lokacin Boko Haram sun shigo Adamawa.”

Wannan magana na kare kai ba karamin hatsari ke tattare da shi ba, muddin kowa zai dauki alhakin kare kan shi, to an yi ban kwana da zaman lafiya kuma kenan. Domin a irin wannan dalili ne ake samun shigo da makamai cikin kasar.

Babbar illar cewa kowa ya kare kanshi shine idan maganar ta fito daga wanda yake jagorantar al’umma. Misali yanzu gwamnan da ya fito ya yi wannan magana na kare kai, tamkar fa umurni yake baiwa jama’ar shi, shine kuma kwatankwacin abinda wancan Faston ya yi.

Daga haka kuma barna ta shigo.

Don haka dole gwamnati ta sake farfado da maganar tsaro a kasar nan. Domin tabarbarewar tsaron ne haddasa kisan mutane a kullu yomin. To ina kenan zamu da wannan bala’i? Domin fa babu gwamnati idan har bab al’umma.

Za a iya samun marubucin akan wannan adireshi:

Kuli_kuli_ba_yaji@gmail.com 

Facebook: www.facebook.com/mahmud.isa.752

Source: LEADERSHIP Hausa