Burina In Yi Fim Da Priyanka Chopra – Rahama Sadau

Rahama Sadau

Rahama Sadau na daya daga cikin ’yan fim din Hausa da ke tashe. Haifaffiyar Jihar Kaduna ce ita. Baya ga kwarewarta wajen wasa kuma ta kasance gwana wajen iya magana da harshen Indiyanci, kamar kuma yadda ta kasance gwana wajen iya taka rawa. A kwanakin baya ne kafar watsa labarai ta intanet, Premium Times ta gana da ita, inda ta bayyana abubuwa da dama da suka shafi rayuwarta da kuma sana’arta. Ga yadda ganawar ta kasance, a sha karatu lafiya:

Abin da ya ja hankalinta ta shiga harkar fim
Tun ina karamar yarinya nake sha’awar fim kuma nake sha’awar in zama ’yar fim. A lokacin da na girma kuma damar shiga fim ta zo mini, ban yi wata-wata ba, kawai sai na rungume ta. Na fara sana’ar fim.

Wadanne irin kalubale ta fuskanta a lokacin da take son shiga harkar fim?
A lokacin da na shaida wa mahaifiyata kudurina na son shiga harkar fim, ba ta so ba, domin kuwa hankalinta bai natsu da harkar ba. Haka kuma, ba ta son in yi nisa daga kusa da ita, kasancewar ta san ’yan wasan fim kan yi tafiye-tafiye zuwa garuruwa daban-daban, har ma da wajen jihohinsu na ainahi, domin daukar shirin fim. Duk da haka, bayan wani lokaci ina ta tuntubawa, sai ta amince mini da in shiga.

Wane fim ne na farko a cikin fina-finan da ta fito a cikinsu?
Fim din ‘Gani Ga Wane’ shi ne na farko da na fara fitowa a cikinsa. Ina kaunarsa sosai saboda na fito cikinsa tare da Ali Nuhu, kuma ba sai na fadada maka bayani ba, ka san abin da nake nufi; a ce mutum ya fito fim tare da Ali Nuhu, a duniyar fina-finan Hausa.

Wane dalili ya sa Ali Nuhu yake burgeta?
A gare ni, Ali nuhu shi ya fi kowane dan wasa burgewa da kwarewa kuma shi ne ubangidana a harkar fim. Shi ya koya mini harkar fim ko kuma ma yake kan koya mini. Na dade ina da burin in ga cewa na fito fim tare da shi kuma sai gashi burina ya cika, fim dina na farko, sai gas hi na fito tare dashi. Ya kasance jarumin jaruman fim, wanda ya dade yana cin kyaututtuka a fagen fim.

Ta kasance ’yar rawa, ko har yanzu tana taka rawa?
A’a. a yanzu na daina yin rawa. Na dauki lokaci mai tsawo da daina rawa.

Ko za ta dawo ta ci gaba da taka rawar Indiyawa?
A’a, ba zan ci gaba ba, sai dai kuma a cikin fim. Duk aikin fim din da aka ba ni, idan dai har an bukaci in yi rawa a wata fitowa, zan taka ta sosai, daidai iyawa ta.
Wane fim ne ya fi ba ta wahala cikin fina-finanta?
Fim din da ya fi ba ni wahala, kuma na fuskanci babban kalubale a kansa, shi ne ‘Dogon Zamani.’ Fim din yana cike da kalubale, domin kuwa furodusansa yana son ganin komai ya zama ingantacce a cikinsa. Dalilin haka ya sanya muka wahala kwarai wajen shirya shi.

Wane shirin fim ta fi sha’awar fitowa?
Ni na fi son in fito a cikin fina-finai masu ilimantarwa da nishadantarwa. Haka kuma ina son fim mai dauke da rawa da waka.

Wane dan wasan waje take son yin fim da shi, idan ta samu dama?
A rayuwata, ina son haduwa da ’yar fim din Indiya, Priyanka Chopra. Don haka idan na samu dama, ina son in yi fim tare da ita. Idan na samu want ton dama, lallai burina ya cika.

Wane dan fim ya fib urge ta cikin ‘’yan fim din Kudancin Najeriya?
‘’Yar wasar da ke matukar burge ni a Kudancin Najeriya, it ace Tonto Dikeh.

Wane fim ne ya fi burge ta?
Fim din ‘Sabon Sangaya’ shi ya fi burge ni. Ina matukar sha’awar fim din, duk da cewa bai kai ga fitowa kasuwa ba.

Cikin mawakan fina-fina Hausa, wane ne ya fi burge ta kuma ta fi so?
Nazifi, Umar da Nura.

Ko wadanne bangarori take son ta ga an bunkasa a fina-finan Hausa?
Duk wani al’amari na rayuwa yana son a bunkasa shi kuma a inganta shi. Saboda haka, ina ganin akwai bukatar tallafi daga gwamnati. Idan aka samu wannan tallafi, za a samu bunkasa shi.

Wane irin abinci ta fi so?
Na fi sha’awar Sakwara.

Asali: Aminiya

Source: Muryar Arewa