‘Da ‘yan Niger cikin ‘yan taddar da ke yakar jamhuriyar’

Babban jami’in kula da hukumar zaman lafiya ta jamhuriyar Niger, Kanar Abu Tarka ya ce akwai sa hannun ‘yan kasar wajen kai mata hare-hare da kungiyar ‘yan ta’adda ta Mali wato Mujao ke kai wa jamhuriyar.

Ya ce da wasu ‘yan Niger da suka tsallaka Mali ake kitsa hare-haren.

Yankin Tillaberi dai na fuskantar hare-haren ta’addanci daga kungiyar ta Mujao, al’amarin da ya sanya gwamnati ta ayyana dokar ta-baci har na tsawon watanni uku.

Tuni dai hukumomin kasar suka yi kira ga mazauna yankin Tillaberi da ke iyaka da kasar Mali da su bai wa jami’an tsaro hadin-kai ta hanyar sanar da su duk wata bakuwar fuska da suka gani.

Hukumomin sun ce nuna bakin fuskokin, zai taimaka wajen yaki da ta’adancin da kasar ta sa a gabanta.

Gwamnan jihar Tillaberi, Ibrahim Kachalla wanda ya yi wannan kira, ya ce yankin na fama da hare-haren sari-ka-noke daga ‘yantawaye na kasar Mali.

Jamhuriyar Niger dai na tsaka mai wuya sakamakon hare-hare daga kasashe masu makwabtaka da ita.

Kungiyar Boko Haram daga Najeriya da kuma Mujao da ke Mali na kai wa jamhuriya munanan hare-hare da ke sanadiyyar mutuwar mutane da jami’an tsaron kasar.

Source: BBC Hausa