Dokokin shige da fice za su taimaka wa tsaro a Nijeriya

Hukumar kula da shige da fice ta Nijeriya ta kaddamar da sabbin dokokin shige da fice da nufin inganta harkokin tsaro da karakainar baƙi a ƙasar.

Dokokin za su taimaka wajen bibiya da inganta tsaro da kuma bayar da dama ga ‘yan kasuwa daga kasashen waje shiga Nijeriya domin gudanar da harkokinsu ba tare da tsangwama ba.

Ministan cikin gida na Nijeriya Laftanar Janar Mai ritaya Abdulrahaman Dambazau shi ne ya sanar da hakan bayan kaddamar da wadannan sabbin dokoki da suka fara aiki nan take.

Ministan ya sanar da irin tasirin da wadannan dokoki za su yi ga rayuwar ‘yan Najeriya ta fannin inganta tsaro da kuma baƙi ‘yan kasuwa.

”Za su karfafa harkokin tsaro a kasa kuma su ba da dama ga wadanda ke son shiga ƙasar don kasuwanci, ko wani abu daban su samu wannan damar ba tare da wahala ba”

Ministan ya kuma ce dokokin da aka sanya wa hannu tun a shekarar 1963 ba a sake waiwayarsu ba sai yanzu, kuma an yi hakan ne saboda abubuwa sun sauya, abubuwan da ake yi da ba su ake yi a yanzu ba.

Sabbin dokokin sun yi tanadin kwana 80 ga bakin da za su shiga Nijeriya in ji Muhammed Babandede shugaban hukumar kula da shige da ficen ta Nijeriya.

”Duk wani wanda zai shigo ko daga kasashen ECOWAS ne wato Afirka ta Yamma, yana da ikon zuwa Nijeriya ba tare da visa ba har ma su kafa kasuwancinsu.”

Ga alama sauyawar zamani na daya daga cikin dalilan da suka sanya aka yi gyaran fuska ga ƙa’idojin shige da ficen na Nijeriya.

Source: BBC Hausa