DRC: Rikici ya barke a yankin Kivu

An dai dauki lokaci ana rashin zaman lafiya tsakanin kabilun kasar, da ake asarar rayuka da dukiya

Rahotanni daga yammacin jamhiriyar dimukradiyyar Congo na cewa akalla mutane ashirin da biyar aka hallaka, a lokacin da wasu kungiyar masu dauke da makamai suka kai hari wani kauye a kasar.

‘Yan siyasar arewacin yankin kivu, sun shaidawa BBC cewa wasu da ake zargin ‘yan kungiyar Mai-Mai Mazambe sun afkawa kauyen dauke da adduna da barandami, inda suka dinga saran fararen hula da suka gani.

Mutanen da lamarin ya rutsa da su dai ‘yan kabilar Hutu ne, wadanda fiye da shekaru goma kenan da ake tashin hankali tsakanin kabilun kasar da aka fi kashe kabilar da Hutu.

Jama’a dai sun yi ta gudun ceton rai, a lokacin da lamarin ya faru an yi kuma ta rufe gidaje saboda tsoron kar su afkawa iyalai.

Source: BBC Hausa