FAHIMTA FUSKA: Sheikh Ibrahim Khalil

A aiko da tambaya ta wadannan imel: shafinfahimtafuska@yahoo.com ko leadershiphausa@yahoo.com ko kuma sakon ‘text’ ta wannan lamba domin Malam ya amsa tambaya: 08096972247, 07013495497.

Assalam Malam, game da amsar da ka bayar cewa, Ibin Taimiyya na daya daga cikin Malaman da ya baiwa Mauludi kariya, a tawa fahimtar gaskiya baka fahimce shi ba ne. Dalilina shi ne yana daya daga cikin sahun Malaman da suka bada fatawar cewa, Mauludi bidi’a ne kai tsaye. Kazalika maganar lada da ka ce ya ce za a samu idan aka yi Mauludin don Annabi, a wane littafi ya fadi hakan?

A,  to tunda baka san littafin da aka yi magana a ciki ba, yaya za a yi ka ce ba a fahimci Ibin Taimiyya ba? idan ka ce ba a fahimci mutum ba, dole ne da farko dai ya zamana ka karanta abin da shi din ya fada a littafin nasa. A nan abin da na fahimta shi ne, tunda ba ka son Mauludi, kana kuma son Ibin Taimiyya, shi yasa kake ganin ba za a ce Ibin Taimiyya ya fadi haka ba, abin da nake so ka fahimta a nan shi ne, shekaru sama da ashirin da suka wuce akwai masu irin wannan ra’ayi nakan wadanda su ma suka musunta hakan, har wasu ma na ganin cewa an yi wa Ibin Taimiyya karya ko kage ko kazafi, don haka ba wai kai ne mutum na farko da ya fara musunta wannan ba. Amma ko shakka babu Ibin Taimiyya ya fadi a cikin littafinsa cewa, Mauludi bidi’a ne makaruhiya, amma idan mutum ya yi don Annabi, yana da lada mai girma don wannan son Annabin. Amma fa yin aikin babu wanda ya sa shi, niyyar ita ce za ta sa a ba shi ladan don kuwa ya yi ne saboda Annabi (SAW), sannan aikin da ya yi bidi’a ce makaruhiya, in ji shi. Ga shi nan a cikin littafin nasa mai suna ‘I’ikida’us suradalmustakima’, ka nemi littafin ka karanta ko ka tsuguna gaban Malaminka ya karanta maka ya fassara.

Malam mene ne hukuncin kayyade iyali?

Babu laifi, ya halatta mutum ya kayyade iyali ya ce, ‘ya’ya biyu zai haifa ko uku ko hudu ko biyar ko kuma sama da haka, ma’ana ya kayyade adadin ‘ya’yan da yake so ya haifa. Ko kuma ya ce zai rika jinkiri idan ya haifi da daya, sai bayan shekara kaza zai sake haihuwar wani dan, wannan babu wani laifi. Inda laifin yake shi ne, idan aka bayar da umarni cewa kowa ya je ya kayyade nasa iyalin. Misali, a ce kowa kada ya wuce ‘ya’ya daya ko biyu, wannan shi ne abin da Malamai ba su yarda da shi ba, ma’ana Hukuma ta bada umarni cewa, kada wanda ya yarda ya wuce ‘ya’ya daya ko biyu ko uku, wannan ne jamhurin Malamai ba su karba ba. A zo a tilasta kowa da kowa kamar yadda wasu kasashe suke yi, duk da cewa idan aka dubi wasu ka’idoji, wata lalura za ta iya sawa Hukuma ta dakatar da haihuwa na shekara daya ko biyu ko uku ko hudu ko ma goma, amma a sa doka ta har abada, a nan matsalar take, sai dai mutum a kansa shi kadai ya zabi ‘ya’ya uku ko biyar ya yi daidai babu laifi. Sannan babu laifi kamar yadda Imamu wakilu ya fada a cikin littafinsa ‘Kitabuzzuhdi’ cewa babu laifi mutum ya ce ‘ya’ya kaza kawai yake so ya haifa ko kuma ya ce kamar yadda wasu Malamai suke fada, ba da tazarar haihuwa (spacing), wannan mutum a karan kansa zai iya yin haka.

Salam Malam, maganar da ka yi cewa, Shehu Usman Dan Fodio, ya yi rabe-raben bidi’o’i, ai ba shi ne wanda ya fara ba, farkon wanda ya fara Bamalike ne wanda tun a wancan lokacin ‘yan’uwansa Malikawa suka yi masa raddi da Hadisin Annabi (SAW) da yake cewa, “Kullu bidi’atun balala wa kullu balalatun finnar”. Saboda haka shi kan sa Shehu Dan Fodio ya dogara ne da ainahin wancan Malamin da tuni ‘yan’uwansa suka riga suka yi masa raddi.

To a nan ai abubuwa ne guda biyar, na farko dai shi wannan Malami na Malikiyya sunansa Izzu Ibin Abdussalam wanda ake yi masa lakani da ‘Suldanul Ulama’, shi ne wanda ya yi wannan kashe-kashe. Sannan shi Izzu wasu sun ce Bashafi’e ne wasu kuma sun ce Bamalike ne, ma’ana Malikawa na sa shi a cikin su, Shafi’awa na sa shi a cikin su kowa na da’awar cewa nasa ne.

Za mu Ci gaba a makon gobe

Source: LEADERSHIP Hausa