FAHIMTA FUSKA: Sheikh Ibrahim Khalil

A aiko da tambaya ta wadannan imel: shafinfahimtafuska@yahoo.com ko leadershiphausa@yahoo.com ko kuma sakon ‘tedt’ ta wannan lamba domin Malam ya amsa tambaya: 08096972247, 07013495497.

To ai ba duk Farfesa ne ya iya rubutu ba, mafiya yawan ‘yan Sakandire ma sun fi wasu Farfesan da dama iya yin rubutu mai kyau. Don haka iya rubutu ba wani abu ne mai muhimmi cancan ba, fahimta da ilmi su ne mafi muhimmanci. Misali, Ibin Hajar wanda ya yi sharhin Buhari Fatahul Bari, bai iya rubutu sosai ba, ga Ibin Taimiya, shi ma ba kowa ne yake iya karanta rubutunsa ba. Sannan idan ka dubi rubutu irin na da, gani za ka yi kamar wani watsattsale-watsattsale ne, wanda a wancan lokacin gani ake yi shi ne rubutu. Saboda haka abu mafi muhimmanci shi ne, ka tabbatar idan ka yi rubutu kai da kan ka za ka iya karantawa sannan idan wani ma ya gani zai iya karantawa.

Sai abu na biyu kuma, ka tabbata ka fada wa malamanka matsalar da kake da ita na rashin iya yin rubutun a cikin jama’a, musamman a lokacin jarrabawa. Amma abin da ya fi muhimmanci shi ne ka daina sawa zuciyarka wannan tunanin na fargaba ko tsoro don kuwa idan ba ka yakice su ba, babu yadda za a yi ka kubuta daga halin da kake ciki. Abin da na fahimta da kai shi ne, babban abin da yake damunka, tsoron ka da ka yi kuskure a rubutunka ko kuma kada a ce rubutunka ba shi da kyau, saboda haka kada ka tayar da hankalinka a kan haka wannan ba wata babbar matsala ba ce.

Assalam. Malam, sau da yawa idan na yi mafarki sai na ga abin da ya faru a farke, yin hakan wani abu ne Malam? Don abin na matukar ba ni tsoro kwarai da gaske.

Mutum ya yi mafarki ya ga ya tabbata, wannan ba wani abu ba ne da za a iya jin tsoro kawai ya danganta da yanayi, wani lokaci mafarkin naka na iya dacewa  yanani na wani abu da zai afku, na biyu kuma wasu lokuta shi kansa shaidan idan yana so ya halakar da mutum idan ya hango wani abu da zai faru, yakan zo ya sawa mutum a cikin barcinsa, shi kuma mutum da ya ga wannan a cikin barci ya afku, a hankali yau da gobe sai ya rika ganin kamar wata daraja ce da shi daga nan sai ya fara jiji da kai ko jin ya isa ko kuma ya rika baiwa kansa wata daraja ta daban, inda daga bisani za ta kai ga lokacin da shaidan din zai iya halakar da shi. Daga nan ne za ta kai ga idan ya yi mafarki a bin bai afku ba sai ya fara tuhumar kansa cewa kaza ko kaza.

Don haka idan mutum ya yi mafarki ya ga abin ya tabbata, wasu lokuta zai iya zama Allah ne ya nuna masa cewa kila ya yi wani abin kirki, Ya karrama shi da wannan, wasu lokutan kuma zai iya zama shaidan ne, idan ya yi mafarki abin ya afku sai rika cewa ai ga shi abin ya afku daga nan ya fara jin wani abu a ransa. Saboda haka muhimmin abu shi ne, idan mutum ya yi mafarki kada ya dauki abin da muhimmanci ya dauka cewa dabi’a ce kawai ta rayuwa, kodai daga Allah ko shaidan ko kuma tunanin mutum, amma mafi yawan lokuta a sa’ilin  da mutum yake cikin nishadi, jin dadi, nutsuwa, farin ciki da kwanciyar hankali ya fi yin mafarki mai kyau, musamman gefannin Sallar asuba, amma idan mutum ya yi mafarki maras dadi ko kyau, ya nemi Allah Ya tsare shi daga sharrin abin da ya gani, idan kuma na farin ciki ne ya yi shiru da bakinsa kada ya fada wa kowa sai masoyansa, idan kuma hayaniya ce kawai ya ja baki ya yi shiru.

Salam. Malam, na samu lalurar kankancewar mazakuta, wannan ya yi sanadiyyar rabuwa da matata, idan sha’awa ta zo min nakan yi amfani da hannuna na biya wa kaina bukata, yanzu haka na samu wata wadda zan aura. Malam ko akwai wani magani da za a taimaka min da shi?

Da ma ai wannan dalilin ne ya sa ake yi wa mutane kashedi, don mutum ya shiga cikin matsi da sha’awa sai ya rika wasa da mazakutarsa saboda ya fitar da maniyyi, shi ne abin da ake ta jan hankalin mutane su daina musamman samari don gudun fada wa irin wannan hali. Da yawa akwai samari da matasa da ba sa jin magana wanda hakan yakan yi sanadiyyar fadawarsu irin wannan hali da ake yi musu kashedi a kai. Abu na biyu kuma, ba a san inda kake ba ballantana a taimaka maka da wannan magani, amma shawarar da za a ba ka ita ce, ka daina wannan abin da kake yi , ma’ana dole ka daina yin wasa da zakarinka saboda shi ne ya jefa ka a wannan yanayi da ka samu kan ka.

Sannan ka rika shan zuma babban cokali kafin ka ci abinci da safe, haka da rana da kuma dare duk dai kafin ka ci abinci. Haka zalika kafin ka kwanta barci ka sha cokali biyu ko uku sannan ka kwanta, haka za ka yi ta yi har zuwa tsawon wani lokaci.

Assalam. Malam, mata na cin ‘ya’yan itatuwa kamar karas, ayaba, kankana, lemu da sauran su. Malam mu kuma maza me ya kamata mu yi amfani da shi?

Ku ma maza abin da za ku rika yin amfani da shi kenan, sannan ku rika cin kaza amma ba koda yaushe ba, kazalika ku rika shan abarba ita ma za ta taimaka muku kwarai da gaske. Sannan cin naman kazar ba koda yaushe ba, ana iya ci kamar da yamma, Allah Ya sa a dace, amin.

Source: LEADERSHIP Hausa