Gwamna Gaidam Ya Yi Shagube Ga ‘Yan Siyasar Yobe

Ibrahim Gaidam

Gwamnan jihar Yobe, Alhaji Ibrahim Gaidam ya bayyana cewa yana fadi-tashin ganin cewar mutumin da zai gaji kujerar da yake kai idan Allah ya kai mu shekarar 2019, dole ya kasance mutum nagari wanda yake da kyakkyawar manufa ga al’ummar jihar baki daya.

“Saboda haka, ba za mu taba lamunta da mayaudaran ‘yan siyasa ba maras kishin al’ummar mu. Mutanen da bayan mun zabe su a 2015 ba mu sake jin duriyar su ba, duk da yadda muka fada cikin matsaloli kala-kala amma koda sau daya ba su taba jajanta wa jama’ar mu ba; walau a baki ko ta kafar yada labarai. Idan ka gansu wajen mu to lokacin zabe ne, kuma ana gama wa shikenan sun koma Abuja abin su”.

Gwamnan ya bayyana hakan ne ga dubun-dubatar al’ummar jihar a lokacin bukin rantsar da sabbin zababbun shugabanin kananan hukumomin jihar 17, a gidan gwamnatin jihar da ke Damaturu.

A yayin da yake shagube dangane da halayyar wasu da ya bayyana bara-gurbin ‘yan siyasa tare da kira ga jama’ar kan cewa kada su sake su yaudare su da kudi ko dadin baki, ya ce, “Ba al’ummar Yobe ne a zukatan su ba, burin su shi ne su samu mulki don su taka wanda suke su kuma su yiwa dukiyar al’umma wa-kaci-wa-tashi, ina mai tabbatar wa ‘yan siyasa masu irin wannan mafarkin da cewa mulkin Yobe ya fi karfin su, saboda kan jama’a ya waye. Kuma za mu yi duk iya kokarin ganin wanda zai gaje mu ya kasance mutum nagari da son ci gaban Yobe baki daya”.

Har ila yau ya bayyana cewa duk da har yanzu lokaci bai yi ba, amma dole su gaya wa jama’a “kada ku yarda da mashaya wiwi, ko mashaya giya da koken balle kuma ‘yan caca a Legas da Abuja, duk wadannan ba za su samu mulkin Yobe ba. Mai tunanin PDP kam kada ma ku saurare su, sannan kada ku yarda a yaudare ku, ku yi la’akari da masu fada da cikawa”. Ya nanata.

Alhaji Ibrahim Gaidam ya bukaci sabbin zababbun shugabanin kananan hukumomin da su karkata akalar su ga muhimman ayyukan da za su bunkasa rayuwar mazauna yankunan karkara ta fuskar kyautata ilimi, kiwon lafiya tare da habaka aikin noma da dakile ma’aikatan boge da makamantan su.

A cikin zantawar sa da wakilin mu jim kadan da shan rantsuwar kama aiki, shugaban Karamar Hukumar Bade, Aji Saleh Suleiman ya bayyana godiyar sa ga Allah bisa damar da ya bashi ta hidimta ma al’umma. Sannan ya ce, “Kuma zan yi amfani da wannan dama wajen mika godiya ta ga al’ummar Karamar Hukumar Bade; maza da mata, bisa ga cikakken goyon bayan da suke ba ni, kuma insha Allahu za mu yi kokari wajen baiwa marada kunya” in ji shi.

Source: Leadership Hausa