Gwamnan Bauchi Ya Tsige Mai Tallafa Masa Kan Harkokin Dalibai

Gwamnan Jihar Bauchi Muhammad Abdullahi Abubakar ya umurci da a gaggauta dakatar da mai tallafa masa na musamman kar harkokin dalibai, Kwamared Muhammad Ibrahim Jibo nan take a bisa zarginsa da ake yi da aikata manyan laifuka.

Bayanin hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa daga gidan gwamnatin jihar wacce Sakataren Gwamna, Alhaji Bello Shehu Ilelah ya rattaba wa hannu kana aka aike wa ‘yan jarida cikin har da LEADERSHIP Hausa a ranar litinin din nan da ta gabata.

Sanarwar korar ta ce wannan matakin ya biyo bayan rawar da ya taka ne na rashin kangado a tsarin da Gwamnan jihar ya fito da shi don tallafa wa matasa kan ilimi na samar musu da guraben karatu a fadin kasar nan a karkashin shirin Gwamnan na ‘M.A Youth Educational Empowerment’. Bayan wannan, sanarwar ta zargi Jibo da haifar da matsalar da ta-ki-ci-ta-ki-cinyewa ta kukiyar dalibai wato ‘NUBASS’ wadda ta jawo baraka a tsakanin daliban jihar.

Wakazalika Gwamnan Abubakar ya amince da nada kwamiti mai mutane uku da zai yi dubiya kan aiyukan mai tallafa masa na musamman kan bayar da tallafin karatu da wasu muhimman aiyukan da suka shafi ofishin nasa.

A cewar gidan Gwamnati ta bakin sakatarenta Ilaleh, babban sakatare na ma’aikatar  kula da addinai na Jihar Bauchi Muhammad Auwal Ibrahim shi ne zai jagoranci kwamitin don kawo rahoto kan wannan sashen.

Sanarwar ta ce korar nan take ne ba tare da wani bata lokaci ba; a bisa rashin da’a da mai tallafa wa gwamnan ya nuna.

Source: Leadership Hausa