Har yanzu babu wanda ya dace ya gaji kujerata — Mugabe

Shugaban Zimbabwe, Robert Mugabe, ya ce, jam'iyyarsa ta ZANU PF da kuma jama'ar Zimbabwe, ba su ga wani nagartaccen mutum da ya dace ya gaje shi a shugabancin kasar ba, a manyan zabukan da ake shirin yi a 2018.

Shugaban Zimbabwe, Robert Mugabe yana mulki tun 1987

A wata hira da kafar watsa labarai ta gwamnatin kasar gabanin ranar cikarsa shekara 93, Mugabe, ya ce, galibin ‘yan Zimbabwe ba su ga mutumin da ya dace ya maye gurbinsa a matsayin shugaban kasar ba.

Tun dai 1980 shugaban ke mulkin Zimbabwe.

A watan Disamban da ya gabata, jam’iyyar ZANU PF ta tabbatar da shi a matsayin dantakararta a zaben shugaban kasar da ke tafe.

Da man dai rahotanni sun rawaito mai dakin shugaban, Grace Mugabe tana cewa ‘yan kasar za su iya zaben ‘zaben gawar mijinta’.

Kuma a baya-bayan nan ne jiga-jigan jam’iyyar ZANU PF suka sake ba wa shugaba Mugabe damar sake tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar.

A 2018 ne dai ake sa ran kasar za ta gudanar da babban zabenta, a inda kuma za a sake zaben shugaban kasa.

Source: BBC Hausa