Idan mijinki ya mare ki ki rama — Sarki Sunusi

Muhammadu Sanusi

Mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sunusi na biyu ya yi gargadi ga masu dukan matansu, a inda ya ce ya shaida wa ‘yarsa cewa idan mijinta ya mare ta to ta rama.

Sarki Sunusi ya kuma ja hankalin masu rike da sarautun gargajiya kan dukan matansu, a inda ya ce duk mai rawanin da aka samu da laifin dukan matarsa to a bakin rawaninsa.

Muhammdu Sunusi ya kara da cewa a tsarin sarautar Kano duk mai sarauta walau dai hakimi ko dagaci ko kuma mai unguwa har ma limami da aka kai fada yana dukan matarsa to zai ajiye rawaninsa.

Source: BBC Hausa