Jam’iyyar PDP ta yi wa Buhari barka da zuwa

Jam’iyyar PDP da ke hamayya a Najeriya ta yi wa shugaban kasar Muhammadu Buhari barka da dawowa gida daga jinyar da ya yi a Ingila.

Wata sanarwa da PDP bangaren Sanata Ahmed Makarfi suka fitar, ta yi addu’ar Allah ya kara wa shugaban kasar sauki a kan cutar da yake fama da ita.

Ta ce: “Muna yi wa shugaban kasa addu’ar samun cikakkiyar lafiya sannan muna bayar da shawara ga fadar shugaban kasa cewa nan gaba ta daina boye-boye kan rashin lafiyar ta Shugaba Muhammadu Buhari”.

PDP ta yi kira ga ‘yan kasar su ci gaba da yi wa shugaban addu’a domin samun sauki cikin hanzari, sannan ta yaba wa mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo bisa rawar da ya taka bayan tafiyar shugaban jinya.

“Muna yin godiya ga mukaddashin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo kan rikon da ya yi wa mulkin kasar nan a lokacin da shugaba ba ya nan.

Kakakin PDP Prince Dayo Adeyeye ya kara da cewa “muna kira a gare shi ya ci gaba da aikin da yake yi na fitar da kasar nan daga matsanancin halin tattalin arzikin da ta fada a ciki.”

‘Zan koma asibiti’

Shugaba Buhari dai ya ce yana samun sauki sosai, amma watakila nan da makonni kadan masu “ya koma asibiti”.

Ya bayyana haka ne a jawabin da ya yi wa ‘yan kasar a fadarsa da ke Abuja jim kadan bayan saukarsa daga birnin London.

A cewarsa, bai taba kwantawa rashin lafiya irin wacce yake fama da ita yanzu ba.

Shugaba Buhari ya kara da cewa, “Ina matukar nuna godiya ga dukkan ‘yan Najeriya, Musulmi da Kirista, wadanda suka yi ta yi min addu’a, kuma suke ci gaba da yi min addu’ar samun sauki”.

Shugaban na Najeriya ya ce babban abin da zai sanya a gaba yanzu shi ne yi wa ‘yan kasar aiki tukuru domin bayyana musu irin jin dadin da ya yi da addu’o’in da suka yi masa.

Source: BBC Hausa