Alphabet Ya Sake Yiwa Amazon Tazara Da Sabon Na’urar Sa Ta Google Assistant

Kamfanin Alphabet wanda ya kirkiro wata sabuwar na’urar amsa kuwwa ta Google yayi wa Amazon tazarar da wani da tasu na’urar da aka fi sani da Alexa. Sai dai masana na magana kana wacce riba kamfanin Google ke dashi akan takwarar ta wato Amazon?

Kamfanin ya fara rarraba sabuwar na’urar mai sarrafa lamari na gidaje, wani sabon tsari da zai bayar da dama ga Google Assistant ya sarrafa na’urori na gida ta hanyar murya.

Sai dai wani tsokaci a yanzu shine sabuwar na’urar ta Google ta kasance zata iya sarrafuwa ne ta hanyar amfani da na’urar Google Pixel kadai.

Na’urar Google Home amsa kuwwa ce da kan bawa masu ita damar sarrafa kayayyakin amfanin su na gida ta hanyar murya tare da kunna kida dama talabijin baki daya.

Na’urar a yanzu ta kasance amsa ga na’urar Amazon Echo.