Kashi 20 Cikin 100 Na Kudin Nijeriya Jabu Ne – Obadia Mailafiya

Dakta  Obadia Mailafiya, tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Nijeriya, ya ce, kimanin kashi 20 cikin 100 na tsabar kudin Naira da ake kashewa a Nijeriya na jabu ne.

Mailafiya, ya shaida wa manema labarai cewa hakan na barazana ga tattalin arzikin kasar, wanda tuni ya fada mawuyacin hali.

A cewarsa ma’aikatan babban bankin kasar na hada baki da bankunan kasuwanci domin sake dawo da kudaden da suka tsufa cikin sha’anin hada-hadar kudi.

Dakta Mailafiya, ya bayyana hakan ne, a yayin da ya ke jawabi akan bitar kasafin kudin 2017 da aka shirya na kwanaki uku, inda ya babu yadda za a yi a rage kudaden farashin abinci bayan kasar na amfani da kudaden jabu.

Source: LEADERSHIP Hausa