Kebbi Ta Dukufa Wajen Noman Shinkafa Da Alkama

Shekara daya da rabi bayan kaddamar da shirin ba da tallafin noman rani na shinkafa da alkama a Birnin Kabbi mutane da dama ne suka koma gona lamarin da ya sa jihar ta kama turbar samar da shinkafa da alkama da ka iya wadatar da Najeriya.

Garba Muhammad Bindiga Karaye kwamishanan gona na jihar kuma shugaban kwamitin bunkasa noman shinkafa da alkama ya ce wannan manufa da aka shirya Allah ya sa an cimma nasara.

Ya ce burin shi ne a bunkasa kasa da abinci, jama’a su samu aiki kana tattalin arzikinsu ya karu sannan kudaden da ake fita da su sayo abinci su zama an ajiyesu ko kuma a mayar da su wani gefen a yi amfani da su.

A cikin ranin bana za ‘a noma shinkafa wajen tan miliyan 2.5, sannan akwai manoma 3000 masu kadada guda guda da suka shiga aikin. hade da kuma manyan manoma wajen 3000.

Source: VOA Hausa