Kimiyya: Za a gudanar da zanga-zanga a Amurka

Gwamnatin shugaba Trump na shan suka saboda manufofin ta da ba sa yi wa wasu dadi.

Shugaban kungiyar masu bincike mafi girma a duniya, ya nuna goyon bayansa kan wata zanga-zanga da aka shirya yi a birnin Washington saboda matakin da shugaba Trump ya dauka na nuna rashin amincewa da binciken kimiyya.

Shugaban kungiyar Rush Holt ya bayyana goyon bayan shi ga gangamin da za a yi a watan Afrilun shekarar nan, a wajen wani taro da kungiyar ke yi duk shekara a Boston.

Masu binciken kimiyyar sun nuna rashin jin dadi, kan kalaman mista Trump da ya musanta matsalolin da ake fuskanta sanadin dumamar yanayi.

Harwayau, ana zargin gwamnatin Amurkar da takaita samun bayanai daga cibiyoyin kasar don tabbatar da sun zo daidai da tsarin fadar White House.

Source: BBC Hausa