Kotu ta mallaka wa gwamnati dalolin Andrew Yakubu

Andrew Yakubu ya rike matsayin shugaban NNPC daga shekarar 2014 zuwa 2014

Wata babbar kotun tarayyar Najeriya da ke zamanta a jihar Kano ta mallaka wa gwamnatin Najeriya naira biliyan uku da aka gano a gidan tsohon shugaban kamfanin mai na kasar, NNPC.

Hakan ya biyo bayan bukatar da hukumar da ke yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati ta EFCC, ta shigar a gaban kotun.

A ranar Talata ne kotun ta bayar da umarnin cewa kudin da suka kai kusan $10 da kuma fam 750,000 da aka gano a gidan Mista Yakubu da ke Kaduna sun zama na gwamnatin Najeriyar.

Umarnin kotu

Kotun wadda mai shari’a Zainab Abubakar ke jagoranta, ta bayar da wannan umarni ne a matsayin na wucin gadi har sai lokacin da aka kammala shari’a a kan batun kudaden.

Ko da yake ya zuwa yanzu ba a kai ga gurfanar da Mista Yakuba ba tukuna a gaban kotu a kan batun kudaden da aka samu a gidan nasa.

Sai dai kawo yanzu tsohon shugan na NNPC na tsare a hannun hukmar ta EFCC wanda ke ci gaba da bincike a kansa.

A makon da ya gabata ne shugaban riko na hukumar EFCC, Mista Ibrahim Magu, ya shaida wa majalisar wakilan kasar cewa sun samu kusan dala miliyan 10 da kuma fam 750,000 a gidan tsohon shugaban kamfanin mai na NNPC, Mista Andrew Yakubu, a yayin da suka kai wani samame.

An kiyasata yawan kudin a matsayin naira biliyan uku.