Makarantar Al’ameen ta yaye dalibai 15 da suka sauke Alkur’ani

Makarantar Madarasatu Ameenul Islamiyya wadda aka fi sani da Al’ameen da ke Hayin Banki, a Kaduna ta yaye dalibai 15 da suka hada da maza biyu da mata 13 a ranar Lahadin da ta gabata a dakin taro na Arewa House da ke Kaduna.

Da yake jawabi a wajen taron, shugaban makarantar, Malam Yusuf H. Bello ya gode wa Allah da Ya nuna masa ranar da yake yaye dalibansa, inda ya yaba wa malamai da daliban da suka sauke Alkur’ani Mai girma kan jajircewar da suka nuna.
“ Yana daga cikin burina in ga jama’a sun samu ilimin addini da na zamani tare da tarbiyya mai kyau. Wannan ne ya sa na dage wajen tabbatar da cewa na kafa wannan makaranta. Don haka na gode wa Allah da Ya cika mini burina yau ga shi makarantar tana saukar da dalibai karo na shida. Wannan ba karamin abin farin ciki ba ne, ina fata Allah Ya sa wa karatun yaran albarka,” inji shi.
Da yake gabatar da wa’azi a wajen taron walimar, Sheikh Nuhu Tamburawa ya ce Allah Ya halicci mutum ne mataki-mataki, don haka kowane hali mutum ya shiga, bai da wata mafita face ya koma ga Allah. “Maganin halin da muke ciki ba wani abu ba ne mai wahala. Allah Ya nuna mana karara cewa duk wanda ya ji tsoron Allah, to Allah zai ba shi mafita,” inji shi
Aminiya ta zanta da Malam Mubarak Jamilu Wakili daya daga cikin wadanda suka jagoranci shirye-shiryen saukar, inda ya taya daliban murnar hawa wannan babban mataki a rayuwa, ya ce ba kowa ne Allah ke ba wannan darajar ba, don haka yana taya su da addu’a Allah Ya sa tsoron Allah a ciki, kuma Allah Ya yi musu albarka.
Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai Babban Limamin Masallacin Juma’a na Hayin Banki, Malam Is’hak Ibrahim da Sarkin Hayin Banki, Malam Mahmud Galadima da Farfesa Muhammad Tanko da Honorabul Gambo Abdullahi Acro da Sheikh Nuhu Tamburawa, Sheikh Buba Luwa da iyayen dalibai da tsofaffin daliban makarantar da sauran abokan arziki.