Matan Arewa Na PDP Sun Mara Wa Modu Sheriff Baya, In ji Hajiya Kulu Rabah

Hajiya Kulu Rabah

Wata hadaddiyar kungiyar Matan Arewa da ke goyon bayan jam’iyyar PDP a Nijeriya sun bayyana zahirin goyon bayansu, tare da amincewa ma tafiya ta Shugabancin na Sanata Ali Modu Sheriff bayan da wata kotun daukaka kara da ke Fatakwal a jihar Ribers ta tabbatar masa da shugabancin jam’iyyar na kasa.

Jagoran Majalisar Matan Arewa ta ‘Women In Politics’ yankin Arewa, Hajiya Kulu Rabah ce ta bayyana ma ‘yan jarida hakan a cikin makon nan.

Hajiya Kulu Rabah ta bayyana hukuncin da kotun ta yi akan tabbatar da halaccin shugabancin jam’iyyar PDP ga Sanata Ali Modu Sheriff da cewa shi ne al’amari mafi alheri da kyautatawa don ceto jam’iyyar PDP daga rugujewa.

Hajiya Kulu ta kuma bayyana goyon bayan mata ‘yan siyasa daga Arewacin Nijeriya ga shugabancin Sanata Modu Sheriff  sakamakon irin nuna kwazonsa da gaskiyarsa ga neman hadin kai da ciyar da PDP a gaba, duk da irin matsin lamba da taron dangi da ake yi masa.

Hajiyar ta ce, “hukuncin da kotun ta yi ba shakka ya yi daidai kuma akan kima don ganin an ceto mana jam’iyyarmu daga ‘yan baranda, dalilai da ke son amfani da mukamansu bisa tilas na sayar mana da mutuncin siyasa da jam’iyya ga wasu iyayen gidansu da suke yi wa dillanci a jam’iyyar APC ta gwamnatin tarayya.”

Hajiya Kulu Rabah, wacce ta taba  rike mukamim shugabar mata ta jam’iyyar PDP a jihar Sokoto, ta nuna takaicin ganin yadda wasu dattawan jam’iyyar PDP a matakin kasa suka rufe ido suna bin hanyoyin wargaza hadin kai da ci gaban PDP saboda dan abin cefane da bai taka kara ya karya ba.

“Hakika ba shakka ko daya mun san da cewar, Sanata Modu Sheriff shi ne halattaccen shugaban jam’iyyarmu ta PDP tun da farko; yanzu kuma kotu ta tabbatar masa, ya dace ga masu yin jayayya daga gefen Sanata Ahmed Makarfi su yi wa kansu kiyamul-laili su aje wannan jayyayar su zo a yi tafiya daya ga hadin kai don ganin an ceto kasar nan daga mugun mulkin wahala da masifar da aka jefa talakawa,” in ji Hajiya Kulu Rabah.

Dangane da hakan, Hajiya Kulu ta kara tabbatar da goyon bayan Mata ‘yan siyasa daga Arewacin Nijeriya ga wannan hukuncin, da kuma yi masa fatan alheri ga shugaban Modu Sheriff, tare da kira gareshi na ya nemo hanyar tuntuba da kuma sassantawa ta gaskiya da za ta hada kan dukkan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP tun daga matakin mazabu har zuwa kasa baki daya.

Inda ta ce Hakan zai taimaka ga farfado da mutunci da kwarjinin PDP daga irin yanayin da ‘yan jari hujja masu amfani da kudade wajen nuna karfi ga shugabancin jam’iyyar a matakin jihohi da Kananan Hukumomin mulki da na kasa.

Tare da: Abdulrazak Yahuza Jere

08039216372

Source: LEADERSHIP Hausa