Mosul: Yadda aka yi ruwan bama-bamai a fagen daga

A karshen makon da ya gabata ne kimanin mazauna birnin Mosul 2,500 suka tsere daga Yammacin birnin, wanda ke karkashin ikon kungiyar da ke ikirarin kafa daular Musulunci IS, na tsawon shekara uku.

Kungiyoiyin bayar da agaji sun yi kiyasin cewar kimanin mutum 750,000 aka yi wa kawanya a Yammacin Mosul, wadanda suka kasa tserewa daga birnin, duk da cewa akwai yiwuwar nan gaba a yi ba-ta-kashi mai tsawo na neman iko da birnin tsakanin dakarun gwamnatin Iraki da mayakan IS.

Zuwa yanzu hare-haren da ake kai wa a Yammacin Mosul sun yi tsanani kamar yadda aka zata — sojojin Iraki wadanda suka samu isasshen horo da kuma wadatattun kayan yaki suna dannawa cikin birnin, domin karfinsu da kuma hare-hare sama na dakarun kawance da ke taimaka musu.

Duk da musgunawa mutane da mayakan IS ke yi da rashin hakurinsu, suna nuna tsagoran basira a yakin, ta inda a baya-bayan nan suke kaddamar da dabarun yakin da kusan ba a taba amfani da su ba a duk wani yaki da aka taba yi na cikin gari a zamanin nan. Suna amfani da jirage marasa matuka inda suke jeho bama-bamai da gurneti kan fararen hula da sojoji.

Hakika rundunonin soji a gabas ta tsakiya sun yi amfani da manyan jirage marasa matuka wanda galibinsu ke haddasa asarar rayuka.

Amma yawan hare-hare da kuma yadda mayakan IS ke sarrafa kananan jirage marasa matukan wajen kai hare-hare bam a Mosul, yasa dakarun gwamnati sun jinkirta dananwar da suke yi cikin birnin.

Jirage marasa matukan kuma sun sa fararen hula, ciki har da mazauna gabashin Mosul, gigicewa. An kwato wannan bangaren birnin daga mayakan IS a watan jiya a matakin farko na yakin korar masu kaifin kishin Islaman daga sansaninsu na karshe a Iraki.

A wani asibiti a brinin Irbil da ke arewacin Iraki, wakilin BBC ya hadu da Umm Mohammed mai shekara 55, tana kuma da ‘ya’ya bakwai, wadda ‘yar asalin gabshin Mosul ce, tana zaune ne kan gadon asibiti inda ake sa mata ruwa. Ba ta iya kwanciya saboda tsananin ciwon da kafarta ta dama ke yi.

Ta ji rauni ne a kafarta sakamakon fadowar bam daga jirgi marasa matuki.

Ta bayyana wa wakilin BBC cewar: “Na je kasuwa ne kawai in yi wata sayayya… Kawai sai na ji ina kwance a kasa ina kallon sama. Mutane suna ishara da zuwa sama inda bam din ya fado. Ina jami’an tsaro lokacin da wadannan jiragen ke shawagi a sama suna kashe mu?”

Tasirin hare-haren a halayyar mutane

Amfani da jirage marasa matuka da kuma araharsu ba za su sauya yadda rikicin nan ke tafiya ba.

Akwai dubban makamai wadanda suka fi tsada da hatsari wadanda ake kaddamarwa kullum a wannan rikicin.

Duk da haka ba za a iya kore tasirin amfani da jirage marasa matuka da ake amfani da su a rikicin ba, inji Emanuele Nannini daga hukumar bayar da agajin gaggawar Italiya, wadda ke kula da asibitin da Umm Mohammed da kuma sauran wadanda hare-haren bam din jirage marasa matuka suka shafa ke samun kulawa.

“A zahiri, daya suke da harin roka, amman sun fi samun inda aka harba su,” inji Mista Nannini, wanda ya fadi haka a lokacin da yake sa ido a shirin gaggawa na fadada gadaje da kuma dakunan asibitin domin yakin da ake yi a yammacin Mosul.

“Saboda haka ko wanne daga cikin jirage marasa matukan nan na samun inda aka yi hako. Ta fannin halayya abu ne mai wuya ga mutane saboda za su iya kai hari a ko wani lokaci da kuma ko wani wuri,” inji shi.

Mazauna gabashin Mosul suna samun hutun kankanin lokaci daga hare-haren jirage marasa matukan saboda mayakan IS sun mayar da hankalinsu kan sabbin fagen yaki a kudanci da yammacin birnin.

Kwamandan runduna ta daya ta sojin dawakin Amurka Laftanar Kanar John Hawbaker, “Yakin Mosul zai kasance babban kalubale ga ko wacce rundunar soji, amman wannan yakin zai kare ne kawai da sakamako daya.”

Suna kuma samun taimako da shawarwari daga dakarun kawance na wasu kasashen.

A sansanin da wakilin BBC ya ziyarta kilomita kadan daga yammacin Mosul, manyan tankokin Amurka masu sulke sun harbi mayakan IS a ciki da kusa da birnin da aka yi wa kawanya.

Source: BBC Hausa