‘Mutane da yawa ba su san suna da makanta ba’

Wani bincike da aka yi kan cutar dusashewar gani wato Glaucoma, a Najeriya, ya nuna cewa mutane da dama na da cutar ba tare da sanin suna da ita ba.

Binciken dai ya nuna cewa kashi biyar cikin dari na masu shekara 40 zuwa sama, a kasar na da cutar.

Cutar ta Glaucoma dai tana cin idanuwa a hankali sannan daga bisani ta nakasa su.

Masu wannan matsala dai na farawa ne da rashin gani ta gefe.

Source: BBC Hausa