Rikicin PDP: Jonathan Ya Amince da Bangaren Shariff

Goodluck Jonathan

Tsohon shugaban Nigeria Goodluck Ebele Jonathan a jiya ya amince da bangaren Sanata Ali Modu Shariff a matsayin shugaban Jam’iyyar ta Peoples Democratic Party (PDP) na kasa.

Wannan yazo a dai dai lokacin da bangarori daban daban na PDP wadanda suka hada da bangaren majalisar kasa, gwamnoni, kwamitin dattawa na PDP da sauran manyan jam’iyya suka kada kuri’ar raba gardama akan shugabancin na Sanata Shariff.

Tabbatarwar dai ta afku ne a lokaci da Shariff ya kaiwa Jonathan ziyara ta musamman a gidan sa dake babban birnin Abuja wanda ya tabbatar wa da Shariff cewar PDP bata cikin wani rikici.