Rikicin PDP: Jonathan Ya Goyi Bayan Sheriff, Bangaren Makarfi Sun Sa Zare

Rikicin jam’iyyar PDP ya sake daukar sabon salo tun bayan da Tsohon Shugaban Kasa, Dakta Goodluck Ebele Jonathan ya bayyana cikakken goyon bayansa ga tsagin shugabancin jam’iyyar bangaren Ali Modu Sheriff a makon nan.

Jonathan ya ayyana goyon baya nasa ne yayin karbar tawagar Ali Modu Sheriff a gidansa da ke Abuja, inda aka jiyo shi yana fadin ‘shugabana’. Har ila yau, ya ce jam’iyyar a dunkule take ba kamar yadda wasu ke gani ba.

A zantawarsa da Sheriff, Jonathan ya ce “Muna magance matsalolin da muke fuskanta. Da ma ita siyasa ta gaji bambancin ra’ayi. Hanyoyin da za mu kawo karshen bambancin ra’ayi shi ne zai nuna cewa mu ‘yan adam ne, kuma shugabanni. Ba mu da shugabancin bangarori biyu kamar yadda ake fada, jam’iyyar PDP guda daya ce. Na gana da Sheriff, kuma na gana da sauran. Za mu yi dukkan abinda ya dace don tabbatar da ganin mun kasance a matsayin jam’iyya guda.”

Da yake nasa tsokaci, Sanata Ali Modu Sheriff ya ce ba zai bata lokacinsa wajen biyewa masu kokarin kawo rudani a PDP ba.

“Idan na koma ina sauraron magangansu, ni ma na zama daidai da su kenan. Jam’iyyar PDP daya garemu kuma shugabanta guda ne. Muna iya bakin kokarin don mu zama tsintsiya madaurinki daya. Ba ma son rabuwar kawuna. Ba mu da bambanci, balle shugabancin rikon kwarya,” in ji Sheriff.

Cikin wadanda suka yi wa Sheriff rakiya yayin ziyarar, akwai Mataimakin Shugaban Jam’iyya, Dakta Cairo Ojougboh, Farfesa Olawale Oladipo, Kakakin Jam’iyyar, Bernard Mikko da sauran mukarrabai.

Wannan ziyara dai ta biyo bayan hukunci da kotu daukaka kara ta yanke na tabbatar wa Sheriff kujerarsa, wadda ta janyo hankalin masu fashin baki kan harkokin siyasa, musamman da ake ganin bangaren Sanata Ahmad Makarfi sun yi watsi da hukuncin kotun, inda suka kira taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP, wanda ya gudana ranar Litinin a birnin Tarayya Abuja.

Taron da bangaren Makarfi suka gudanar a gidan gwamnan Ekiti na Abuja, ya samu halartar membobin jam’iyyar PDP a Majalisar Kasa, Kwamitin Amintattu da sauran masu ruwa da tsaki, inda suka nuna cikakken goyon bayansu ga jagorancin Makarfi, hadi da bayyana hukunci kotun a matsayin rashin adalci. Haka zalika, sun sake daukaka kara zuwa kotun kare kukanka, wadda suka ce suna sa ran za ta yi masu hukunci na adalci.

A wata takardar da suka rabawa manema labarai bayan kammala zaman, tsagin Makarfi sun bayyana matsayarsu game hukunci kotun, inda suka amince da daukaka kara zuwa kotun gaba, a cewarsu Makarfin dai shi ne halastaccen shugaban jam’iyyar PDP.

Taron gaggawar wanda aka yi a gidan Gwamnan Ekiti, Ayo Fayose, ya samu halartar Kwamitin Amintattu, Gwamnonin PDP, membobin PDP a Majalisar Kasa, Tsaffin Ministocin PDP, Mataimakan Shugaban jam’iyyar na kasa, Shugabannin jihohi da sauran su.

Da yake karanta takardar makasudin zaman, Tsohon Ministan Yada Labarai, Farfesa Jerry Gana, ya ce: “Masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP sun tsaya tsayin daka waje dora PDP kan tsarin da take na hadin kai, juriya, gaskiya da amana karkashin inuwar shugabancin mutum daya. Watau shugaban riko, Sanata Ahmad Makarfi.

Ya ce: “Ya’yan jam’iyyar PDP sun gama bayyana ra’ayinsu game da abin da ya faru tun a 21 ga watan Mayun shekarar 2016 a baban taronmu na birnin Fatakwal, inda muka nuna kin amincewarmu, muka gabatar da korafi gaban kotun. Wanda ya kawo har 20 ga watan Fabrairun 2017 ba mu daina ba.”

Jerry Gana ya ci gaba da cewa, “Mun kada kuri’armu ta nuna cikakken goyon bayanmu ga jagorancin Sanata Mohammed Ahmad Makarfi, ba gudu ba ja da baya. Makarfi kawai muka sani a matsayin shugaban rikon jam’iyyar PDP.

“A wannan gabar, muna kara tabattar da cewa ba za mu taba saurarawa ba, balle mu mika jam’iyyarmu hannun wadanda sam ba su dace ba, hakan tamkar daukar wuka ne mu dabawa cikinmu.

A nasa bangaren, Sanata Makarfi ya yabawa ‘ya’yan jam’iyyar bisa cikakken goyon baya da suke ba shi. Har ila yau ya ce, lokacin da PDP take kan mulki ba ta hana APC gudanar da ayyukanta, domin suna girmama dimukradiyya, saboda haka su ma babu wanda zai hana su gudanar da harkokinsu.

Shi ma Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ike Ekweremadu, ya jadadda goyon bayansa ga Makarfi, cikin abinda ya bayyana da cewar, kokarin da ake yi na kwace jam’iyyarsa daga hannu tamkar fashi da mamaki ne.

Ya ce cikakken goyon bayan da daukacin masu ruwa da tsaki suke bawa Makarfin ya isa manuniya kan inda jigajigan jam’iyyar suka sa gaba, duk kuwa da hukunci da kotu ta yanke.

A wani labarin kuma, jam’iyyar APC ta musanta zargin da ake yi mata na tana da hannu a rikici abokiyar adawarta PDP, inda suka ce sam, ba su da alaka da Modu Sheriff kamar yadda wasu ke fadi.

Sakataren yada labaran APC, Mallam Bolaji Abdullahi ne ya bayyana hakan ya yin zantawarsa da LEADERSHIP, inda ya ce kwata-kwata ba su da hannu a rikicin.

Tun bayan yanken hukunci kotu wanda ya tabbatar wa da Sheriff shugabancin PDP, ake zargin cewar akwai sa hannu APC, musamman da ake ganin Sheriff tsohon dan jam’iyyar APC ne.

Source: LEADERSHIP Hausa