Sasantawa Tsakanin Gwamnatin Zamfara Da Mahara: Akwai Sauran Rina A Kaba

Mun Yi Haka Ne Don Tsaron Lafiya Da Dukiyar Jama’a —Gwamnati

Abin Da Ya Sa Tun Farko Muka Dauki Makamai —Wasu Maharan

Mun Aje Makamanmu Don A Zauna Lafiya —Shugaban ’Yan Sa-kai

A watannin baya ne gwamnatini jihar Zamfara ta kira wani taro, wanda ya hada da Sarakuna masu fada a ji a bangaren tsaro, da sauran Shugabannin jama’a daga sassan jihar daban-daban, wanda suka hada Kwamandojin sojoji daga da Sokoto, Kwamishinan ‘yan sanda, Kwamandan jami’an tsaro na farin kaya da sauran Shugabannin maharani nan da suka tuba, don Shaida Sasantawar da aka cimma tsakanin Maharan da suka addabi jihar na Fulani da ‘yan-sakai na kowane bangare, inda suka tuba daga aika-aikar da suke yi akan rayuka da dukiyoyin al’uma jihar.

Jim kadan bayan zuwan Mataimakin Gwamnan, Malam Ibrahim Wakala Liman, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin wannan Sasantawa tsakanin Maharan da ‘yan sakai, sai nemi ganawa da Shugaban Sarakunan jihar, Sarkin Zamfaran Anka, Alhaji Attahi Ahmad, shi kuma ya nemi ganawa da wasu daga cikin Sarakunan da hare-haren ya fi muni a yankunansu.

Kafin fara wannan taro na wannan rana, duk wanda ya kai dakin taron fa fahimci lallai akwai wata a kasa, domin a cikin Sarakunan, wani ya fita dakin taron ransa a bace, sai daga baya bayan sun ga wani daga cikin manyan Sojojin da ake zaman da su sannan ya huce ya dawo cikin taron. Wannan abu da ya faru wasu tun daga nan ne suka kafahinci lallai wannan taron sasantawa akwai lauje cikin nadi.

Gwamnatin jihar Zamfara da al’ummar ta dai sun kasance a cikin firgici da razani da tsoro, domin suna fama da wannan bala’i ne tun a shekarar 2011, lokacin da Gwamna Abdul’aziz Yari Abubakar ya hau kan karagar mulki na jihar, amma har yanzu irin wadannan abubuwa na faruwa jefi-jefi a wasu yankunan jihar.

Domin ko a ’yan kwanakin baya, wani gungun da ba a san ko su waye ba sun ta kai irin wadannan hare-hare a Kannan Hukumomin Maru, Maradun, Anka, Bukuyum, Zurmi, Bungudu,Tsafe da Birnin Magaji. Inda maharan ke cin karensu babu babaka wajen Kashe mutane, inda ake tafka asarar dubannen rayuka da dukiyoyi masu yawa.

Wadannan hare-hare ya jawo ma jihar a Zamfara dakilewar tattalin arzikinmu, musamman arzikin noma da ma’adanan kasa da Allah ya albarkaci jihar.

Wakilinmu ya sa ruwaito mana cewa abin da ke daure ma jama’a kai shi ne, me ya sa gwamnati ta zura idano ana ta kashe al’umma, amma ta ki daukar matakin maganin abin? Wannan ya sa Jama’a da dama, da masu zuba Jari suka fara tunanin kaurace wa jihar ta Zamfara. Domin bincike ya nuna cewa tun da Gwamna Abdul’aziz Abubakar Yari ya hau kan mulki babu wani kamfani ko wata kasa da suka zo jihar don zuba Jari, duk da arzikin da Allah ya yi wa jihar na dinbin ma’adanai, wadanda kuma Duniya ke bukatarsu.

Sannan uwa-uba, ga shi jihar Zamfara jaririya ce da ba ta da wasu hanyoyin kudin shiga, wanda wannan matsala ta rashin tsaro ta kara samar da gagarumin ci baya wajen tattalin arziki, walwala da gudanar da addini cikin natsuwa a fadin jihar baki daya.

Haka zalika, al’ummar jihar Zamfara ba su manta da wani sabon salon da su kansu maharan suka fito da shi ba na satar mutane don yin garkuwa da su, inda ta kai ma sun fara satar Sarki mai daraja ta biyu a jihar, watau Sarkin  Bukuyum, wanda suka iske shi har fadarsa kuma suka yi awon gaba da shi. Sannan kuma ga Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar Anka, wanda masu garkuwan suka yi awon gaba da shi, sai da ya yi kwana da kwanaki sannan suka dawo da shi.

Sannan ga wasu Kansiloli har da manyan mutane ma ba su bar su ba. Ga ‘yan kasuwa sama da mutum arba’in ,wannan salon Satar ta sa masu garkuwa da mutanen suna  bukaci Milyoyin Naira kafin su fito da su. Wanda ya sa dole ‘yan Majalisar jihar da Kwamishinoni da masu mukaman siyasa suka kaurace ma kauyukansu don gudun fadawa tarkon masu garkuwa da mutane.

Idan ba a manta ba, a bara ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, da Shugaban Rundunar Sojojin kasar nan, Laftanar Janar TY Buratai, suka suka jagoranci kaddamar da wata runduna ta musamman da za ta dakile wannan ta’addanci, inda kuma wannan hadin gwiwar Jami’an tsaro sun yi ta kokarin samar da tsaro da dakile hare-haren, amma abin ya ci tura. Inda daga bisani wadannan baya suka ci gaba da satar mutane da kuma karkashe jama’a, kisan baya-bayan nan shi ne wanda aka yi a Kananan Hukumomin Maradun, Shinkafi da Maru, wanda mutane da dama suka rasa rayukansu da dokiyoyinsu.

A can baya lokacin da wannan abu ya yi kamari ne sai gwamnatin jihar ta samar da wannan kwamitin da zai sasanta da tawagar Buharin Daji da ‘yan sa-kai, wanda ya zama a karkashin jagorancin Mataimakin Gwamnan jihar, Malam Ibrahim Wakkala Liman. Kuma wannan Kwamitin sulhu, da kuma wancan sulhu da aka yi ta kaiwa da komowa a aiwatar da shi ya samu gagarumar karbuwa a tashin farko, sai kuma yanzu ga shi su wadannan mahara da ‘yan sa-kai suna ta samun matsaloli, inda ko a kwanan nan a Karamar Hukumar Tsafe, a wani kauye da ake kira Magazu, su Maharan suka kai hari har suka kashe mutum hudu.

Kuma a makon shekaran jiya ‘yan wasu kauyukan Karamar Hukumar Tsafen, wadanda suka hada da Garin ‘Yan Waren Daji da Bakebake da Tafkin Kazai, suka hada wata runduna mai karfi domin tunkarar wadannan mahara, wadanda ke zaune a Kauyan Mutu tsakanin wadannan kauyukan, suka yi ayari don tunkarar maharan, inda a nan aka yi kare jiki, biri jini. Don Maharan sun karkashe sama da mutum goma a kauyen Bakebake, an kashe mutum biyu a Wailarai, kuma mutum daya, sai Tafkin Kazai mutun biyu, daga ciki akwai Hami na Gande da Ado Turarai, sauran kuma duk sun fito ne daga ‘Yan Warin Daji.

Saboda haka wadannan hare-hare da suka ki ci suka ya ki cinyewa suna nuni da cewa wannan sulhu da aka yi a gaban dubban mutanen jihar, a gaban jami’an tsaro, to lallai ga dukkan alamu akwai sauran rina a kaba, domin ya bar baya da kura. Kuma ya nuna cewa alkawuran da Fulani suka yi na aje makamai da mikasu ga Hukuma da aka yi a wannan biki da ya gudana a Karamar Hukumar Zurmi a kwanakin baya, kuma a gaban Kwamandojin sojoji da sauran jami’an tsaro, har da shi kansa Gwamna Abdul’aziz Yari, bai amfanar da komai ba illa kara tabarbarwar tsaro a jihar.

Sannan kuma a wani taro da aka yi na baya-bayan nan, shi ma na sulhun a fadar Gwamnatin jihar, Sarkin Zurmi a jawabin da ya yi cikin bacin rai, ya dora wa gwamnatin jihar ne alhakin wannan abu da ke faruwa a jihar, domin gwamnati ta san akwai wannan hanyar sulhu, amma ba ta bi ba, sai da aka yi asarar rayuka. Saboda haka sai Sarkin ya ce, “muna fata Allah ya sa wannna sulhu ya kawo karshen asarar rayukan da ake yi a wannan jiha.”

A lokacin wannan zaman sulhu na baya-bayan nan, akwai wani Bafillatani da ya daga hannusa domin a ba shi dama ya yi magana, amma sai ba a ba shi ba, wannan ya sa har ya ciji yatsa don takaici. Wanda kuma bayan kammala taron ya bayyana wa LEADERSHIP HAUSA cewa, “abin da na so in fadi shi ne, ina kalubalantar ‘yan sa-kai da suke cewa gwamnati ta biyasu diyya, shin a ina Rugarsu take, da shekarunsu, kuma wace asara aka yi masu? Mu ke da dukiya, mu aka yi wa asara, mu ake kashewa, mu ne aka kona ma gidaje, amma su ‘yan sa-kai asara me suke da shi da har gwamnati za ta ba su diyya? Don haka wannan lamari, lallai akwai lauje cikin nadi.”

Daya daga cikin maharan da suka mika mukamansu a wannan sansantawa da aka yi, mai suna Samaila Samaho ya bayyana wa taron cewa dole ne ta sa su suke yin wadannan hare-haren, domin manoma sun cinye Labukan shanu, kuma ‘yan sa-kai duk inda suka ga Bafillatani sai kisa. “Don haka mu ma muka dauki matakin kare kanmu da kanmu, tun da gwamnati ta kasa,” in ji shi.

Ya ci gaba da zargin cewa gwamnati ta maida Fulani saniyar ware, duk abubuwan more rayuwa babu a Rigagensu, “ba mu da madatsun Ruwa inda Dabbobi za su sha ruwa, duk inda Bafillatani  yake a Zamfara an dauke shi a matsayin barawo, sai kawai a tare a kashe a kona, ‘yan sa-kai na cin karensu babu babbaka a kan Fulani. Wadannan abubuwa ne suka sa muka dauki wannan mataki. Amma yanzu mun aminta da wannan sulhu, kuma mun kawo makamanmu, daga yau in sha Allahu babu wani rikici,” in ji Samaho.

Shi kuwa Labaran Chairman, wanda yake kuma shi ne jagoran ‘yan Sa-kai na Dansadau ya bayyana cewa, “gazawar gwamnati ne ya sa muka zamo ‘yan sa-kai don kare kanmu da kanmu. Amma yanzu tun da gwamnati ta nemi a sasanta, mun aje makamanmu, ba sauran fada tsakaninmu da kowa, kuma duk wani dan sa-kai da ke cikinmu ya yi abin da bai dace ba, za mu dauki mataki a kansa.”

Shi ma a nasa jawabin a wurin wannan taro, Gwamna Abdulaziz Yari ABubakar ya bayyana jin dadinsa matuka game da wannan sasantawa da aka cimma. Inda ya zauki alwashin yi wa Fulani madatsun ruwa da makarantu da duk sauran abubuwan more rayuwa. Sannan ya tabbatar wad a jama’ar jihar cewa gwamnatinsa ba ta nuna bambanci tsakanin wata kabila, domin duk daya suke a wajansa.

Shi kuwa cikin nasa jawabin, Kwamandan Sojoji na Bataliya ta Daya M. Abade ya bayyana cewa “mun yi matukar murna da wannan sasantawa, kuma duk wanda ya ki ba da goyan baya, to lallali za mu dauki matakin day a ace akansa. Fatarmu ita ce zaman lafiya a kasa baki daya.”

Wani mazaunin kauyan Kango da ke cikin Masarautar Dansadau, Malam Sani Kango, wanda aka sace masa shanu sama da hamsim, kuma ya kwashe shekara daya yana gudun hijira a Gusau, sannan yanzu haka ya koma gida Kango, shi takaicinsa ya nuna game da wannan sasantawa, wanda shi yana ganin kamata ya yi a hukunta masu lafin, ba wai a sasanta da su ba.

Ya ce, “don haka ni na koma gida duk yadda Allah ya yi a kaina na dauki hukunci, tun da gwamnati ta ki taimaka mana. Domin da kansa Gwamna ya bayyana cewa duk wanda ya rasa dukiyoyinsa za a biya shi diyya, amma mafi yawan wadanda aka yi wa asarar dabbobi da gidaje, ba abin da aka yi masu, amma sai ga shi maharan da ‘yan sa-kai su ake kira gidan gwamnati ana ba su diyya. Muna rokon Allah ya gaggauta kawo mana dauki daga gare shi, amma gwamnati ba ta da niyyar taimaka mana.”

A ban garen Sarakuna kuwa, LEADERSHIP Hausa ta nemi jin ta bakin wasu daga cikin Sarakunan da a yankunansu ne aka fi yawan samun wadannan kashe, amma abun ya ci tura. Sai dai wata majiya mai tushe ta bayyana cewa gwamnati ta sanya wa Sarakunnan takunkumin magana da ‘yan jarida ne

Bangaren kugiyar Miyetti Allah kuwa, Shugabanta na jiha, Alhaji Tukur Muhammad Jangebe ya bayyana wa wakilinmu cewa, “wannan shirin sulhu, babu wanda ya fi mu jin dadinsa. Kuma muna kara kira ga gwamnati da kar ta bari mutane na daukar mataki da kansu, kuma kungiyar miyetti Allah ba za ta lamuci cin zarafin Fulani ba. don haka muna kira ga Fulani da su kasance masu bin doka da oda, duk abin da ba su gane masa ba, su gagauta su sanar da mu, mu kuma mu fada ma Hukuma don daukar matakin da ya dace.”

Shi kuwa Kwamandan jami’an tsaro na ‘Cibil Defence’ na jihar Zamfara, Dabid Abi ya bayyana wa ‘yan jarida a Lokacin da ya ziyarce su a sakatariyarsu ta NUJ da ke Gusau a kwanakin baya, cewa “Sulhu da ‘yan sa-kai da Fulani mahara ba zai sa mu yi sakwa-sakwa da aikinmu ba, kuma yanzu haka muna da labarin cewa wadannan mahara sun baro cikin daji suna zaune a cikin birane. Don haka kodayaushe a shirye muke wajen kare rayukan al’umma. Don haka ma’aikatanmu kodayaushe suna cikin shirin kare al’umma.”

Game da rikicin baya-bayan nan a Tsafe, Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda ta jihar Zamfara, DSP Shehu ya bayyana cewa, “rundunar ‘yan sanda ta samu labarin rikici a kauyukan Tsafe, kuma an tura jami’an tsaro, amma ba mu da tabbacin asarar rayuka muna nan muna bincike.

Source: Leadership Hausa