Home » Archives by category » Rahotanni

‘Yadda mahaifina da matarsa ke azabtar da ni’

‘Yadda mahaifina da matarsa ke azabtar da ni’

Wata matashiya ‘yar shekara 20 ta ce mahaifinta bisa hadin gwiwar matar uba, yana azabtar da ita, a inda har yake yi mata barazanar korar ta daga gidansa. Budurwar wadda ta nemi a sakaya sunanta ta shaida wa Amina Aminu ta sashen BBC Media Action Najeriya cewa mahaifin nata ne ya hana ta ci gaba […]

‘Da ‘yan Niger cikin ‘yan taddar da ke yakar jamhuriyar’

‘Da ‘yan Niger cikin ‘yan taddar da ke yakar jamhuriyar’

Babban jami’in kula da hukumar zaman lafiya ta jamhuriyar Niger, Kanar Abu Tarka ya ce akwai sa hannun ‘yan kasar wajen kai mata hare-hare da kungiyar ‘yan ta’adda ta Mali wato Mujao ke kai wa jamhuriyar. Ya ce da wasu ‘yan Niger da suka tsallaka Mali ake kitsa hare-haren. Yankin Tillaberi dai na fuskantar hare-haren […]

‘Yan Nigeria sun hana jirgi tashi a Birtaniya

‘Yan Nigeria sun hana jirgi tashi a Birtaniya

An kama mutum 17 bayan wata zanga-zanga da suka yi a filin jirgin saman Stansted da ke garin Essex, wadda ta dakatar da tashi da saukar jiragen sama na wucin gadi a ranar Talata. Da misalin karfe 9:30 na dare aka kira ‘yan sanda bayan da wata kungiyar wasu mutane ta shige filin jiragen sama […]

‘Yan kasuwar Sabon Garin Kano sun sake shiga rigima

‘Yan kasuwar Sabon Garin Kano sun sake shiga rigima

‘Yan kasuwar Sabon Gari da ke Kano a arewacin Nijeriya sun gudanar da addu’o’in neman ɗauki sakamakon rashin samun tallafi bayan gobarar da ta laƙume dukiyarsu a bara. Shekara guda kenan bayan wata mummunar gobara da ta ƙone kanti kimanin dubu huɗu a kasuwar da kuma haddasa asarar biliyoyin naira. Wasu ‘yan kasuwar sun ce […]

‘Gagarumin ci gaba’ kan cutar da ta addabi duniya

‘Gagarumin ci gaba’ kan cutar da ta addabi duniya

Wata sabuwar fasahar magani ka iya kare aukuwar bugun zuciya da shanyewar ɓarin jiki ta hanyar kankare kitse mai yawan gaske, a cewar likitoci. Sakamakon gwajin da aka yi wa maras lafiya dubu 27 a faɗin duniya, na nufin nan gaba kaɗan za a iya amfani da shi a kan miliyoyin mutane. Wata cibiya mai […]

Cajin wayar salula ya kashe wani a banɗaki

Cajin wayar salula ya kashe wani a banɗaki

Wani mutum ya rasu sakamakon jan lantarki a lokacin da yake cajin wayarsa a banɗaki, kamar yadda aka bayyana a sauraron wani bincike. Richard Bull ya mutu yayin da cajar wayar iPhone ɗinsa ta taɓa ruwa a gidansa da ke Ealing, a yammacin London. Mai binciken sanadin mutuwa ya yanke hukuncin cewa rasuwar Richard Bull […]

Nigeria za ta yi zaman a yi ta ta ƙare da Afirka ta Kudu

Nigeria za ta yi zaman a yi ta ta ƙare da Afirka ta Kudu

Wani ayarin majalisar wakilan Najeriya na musamman yana kan hanyar zuwa Afirka ta Kudu ranar Litinin don bin kadin `yan kasar waɗanda hare-haren nuna ƙyamar baƙi suka ritsa da su a baya-bayan nan. Ayarin dai na fatan tattaunawa da takwarorinsu ‘yan majalisar Afirka ta Kudu domin lalubo hanyar magance wannan matsala. A makwannin baya ne […]

Kiwo ya rinjayi karatu a Nijar

Kiwo ya rinjayi karatu a Nijar

Hukumar ba da agaji ta duniya ta ce rashin abincin dabbobi a wasu sassa na jamhuriyar Nijar ya sanya rufe kusan kashi 50 cikin 100 na makarantun boko, inda sama da dalibi dubu 33, galibi ‘ya’yan makiyaya suka aske karatu. Hakan na faruwa ne sakamakon wani fari da ake fuskanta wanda kuma ya haddasa rashin […]

Duniya na fuskantar bala’in da ba ta taba fada wa ba tun 1945

Duniya na fuskantar bala’in da ba ta taba fada wa ba tun 1945

Majalisar dinkin duniya ta ce duniya na fuskantar babban bala’in yunwar da rabon ta da fuskantar irin sa tun shekarar 1945, tana mai roko a dauki matakan kauce masa. Babban jami’in bayar da agaji na majalisar Stephen O’Brien ya ce fiye da mutum miliyan 20 ne ke fuskantar bala’in yunwa da fari a Yemen, Somalia, […]

Kotu yanke wa ‘yan sanda hukuncin kisa

Kotu yanke wa ‘yan sanda hukuncin kisa

Wata kotun tarayya a Najeriya ta yanke wa wasu ‘yan sanda biyu hukuncin kisa bayan da ta same su da laifi a kisan wasu ‘yan kasuwa shida a Abuja, babban birnin kasar. Alkalin kotun Ishaq Bello ya ce Ezekiel Acheneje da Baba Emmanuel sun taka rawa wurin kisan matasan ‘yan kabilar Igbo, wadanda ke hanyar […]

Bera ya hana jirgi tashi a London

Bera ya hana jirgi tashi a London

Wani jirgi da ya yi shirin tashi zuwa Amurka daga London ya kasa tashi daga filin jiragen sama na Heathrow, bayan da aka gano wani bera a cikinsa. Fasinjojin da ke cikin jirgin wanda ya yi shirin tashi da misalin karfe 10:40 na safe agogon GMT, don zuwa birnin San Francisco sun zauna tsaf suna […]

Ɗan wanke-wanke ya shiga sahun masu gidan abinci

Ɗan wanke-wanke ya shiga sahun masu gidan abinci

Wani ɗan aikin ɗauko kwanuka ya zama ɗaya daga cikin masu mallakar wani hamshaƙin gidan abinci a duniya. Ali Sonko mai shekara 62, a yanzu ya zama ɗaya daga cikin mutum huɗu da suka mallaki gidan abinci na Noma da ke Copenhagen, wanda sau huɗu yana samun lambar gidan abinci da ya fi kowanne a […]

An Yi Bikin Kaddamar Da Littafin Tarihin Giwar Sarkin Kano

An Yi Bikin Kaddamar Da Littafin Tarihin Giwar Sarkin Kano

A ranar lahadi 19\2\2017 aka yi bikin kaddamar da littafin tarihin rayuwar Uwargidan Mai Martaba Sarkin Kano Mallam Muhammadu Sanusi II, CON mai suna  (Giwar Sarkin Kano), Hajiya Fulani Sadiya Ado Bayero, wanda Sani Ali Kofar Mata ya rubuta. Littafin dai ya kunshi tarihi da gwagwarmayar da Gimbiya Fulani Sadiya Bayero ta yi tun daga […]

Sojojin Najeriya Sun Musunta Rahotan Kungiyar Amnesty International

Sojojin Najeriya Sun Musunta Rahotan Kungiyar Amnesty International

WASHINGTON, DC — Rahotan kungiyar Amnesty International mai rajin kare hakkin bil Adama ta fitar ya nuna cewa sojojin Najeriya na yin kisan gilla ga ‘yan kasar a shiyyar Arewa maso Gabas da kuma masu fafutukar ballewa daga Najeriya a yankin Kudu maso Gabas. Daraktan watsa labarai a hedikwatar sojojin Najeriya, Birgediya janal Rabe Abubakar, […]

Wasu ‘yan bindiga sun kashe sojan jamhuriyar Nijar 15

Wasu ‘yan bindiga sun kashe sojan jamhuriyar Nijar 15

Jami’an tsaro a Nijar sun ce an kashe soja goma sha biyar a wani harin da ake zargin masu da’awar musulunci ne suka kai kan ayarin masu sintiri a kusa da kan iyaka da kasar Mali. Wasu mutane ne dauke da makamai suka kai wa sojojin hari yayin da suke sintiri a yankin Walam cikin […]

Ana fama da yunwa a Sudan Ta Kudu

Ana fama da yunwa a Sudan Ta Kudu

Gwamnatin kasar da kuma majalisar dinkin duniya sun ruwaito cewa wasu mutum 100,000 na fama da matsananciyar yunwa, yayin da mutum miliyan daya kuma za su iya fuskantar fari. ana zargin yaki da tabarbarewar tattalin arziki ne suka jawo lamarin. An sha gargadin cewa za a a yi fama da yunwa a kasashen Yemen da […]

An yi gwanjon wayar tarhon Adolf Hitler

An yi gwanjon wayar tarhon Adolf Hitler

An yi gwanjon wayar tarhon da Adolf Hitler ya yi amfani da ita a lokacin yakin duniya na biyu, kan kudi dala miliyan dari biyu da hamsin a Amurka. Sai dai ba a bayyana sunan wanda ya sayi wayar ba. An gano tarhon mai launin Ja, mai dauke da sunan shugaban Nazi a jiki, da […]

Wata Kungiya Ta Shirya Taron Samarwa Makarantun Jihar Borno Tsaro

Wata Kungiya Ta Shirya Taron Samarwa Makarantun Jihar Borno Tsaro

WASHINGTON DC — Wata cibiyar bincike dake babban birnin tarayyar Najeriya, wato Abuja ta gudanar da taron yini guda da masu ruwa da tsaki kan harkokin ilimi a jihar Borno kan hanyoyin kare dalibai da malamansu daga firamare zuwa sakandare daga hare-haren kungiyar Boko Haram. Kungiyar ta gayyato masu fada a ji kan harkokin ilimi […]

‘Yan Gudun Hijira Sun Koka Akan Ilimin ‘Ya’yansu

‘Yan Gudun Hijira Sun Koka Akan Ilimin ‘Ya’yansu

WASHINGTON, DC — Malam Sani Baga daya daga cikin magidanta kimanin arba’in, wadanda ke samun mafaka a yankin Hotoro, dake Kano, ya bayana yadda yaruwarsa ke fiya da ‘ya’yansa guda ashirin, yace har yanzu batun makarantar shike ci masu tuwo a kwarya. Yanzu haka dai gamayyar ayarin ma’aikatan hukumomin bada agajin a Kano, guda shida […]

Binciken masana ya gano fa’idar cin tsire da kayan lambu

Binciken masana ya gano fa’idar cin tsire da kayan lambu

Jama’a na cin nau’in gashin ne dan jin dadi ko samun dandano a baki, musamman ma dai idan ka na da kudi a lalitarka. To amma yanzu, lamarin ya sauya salo mai ban mamaki wanda kwararru a bangaren kiwon lafiya suka shigo cikin batun gadan-gadan. Tunanin ku su ma sun fara sana’ar ta saida tsire […]

Kun san abin da dalolin Andrew yakubu za su iya yi a Nigeria?

Kun san abin da dalolin Andrew yakubu za su iya yi a Nigeria?

Kwatankwacin hakan dai a kasar shi ne fiye da Naira biliyan hudu. Hukumar dai ta ce ta samu makudan kudaden ne makare a cikin wasu akwatuna masu sulke wadanda wuta ba ta cin su a wani gida a kudancin jihar Kaduna. Shugaban Hukumar ta EFCC, Ibrahim Magu, ya shaida wa BBC cewa “Abin mamaki gidan […]

Bindigogi 661: Wa Yake Son Bala’i Ga Nijeriya?

Bindigogi 661: Wa Yake Son Bala’i Ga Nijeriya?

A duk lokacin da irin wannan abu ya tarar da kai a rayuwarka, zaka nemi tsari daga Allah akan mugun ji da mugun gani, ka tara yawun bakinka waje guda ka tsirtar, sannan ka sake tambayar kanka shin haka lamari yake ne ko kuwa? A wannan watan ne manyan alamu suka nuna cewa akwai wani […]