Home » Archives by category » Shiri Na Musamman

‘Mutane da yawa ba su san suna da makanta ba’

‘Mutane da yawa ba su san suna da makanta ba’

Wani bincike da aka yi kan cutar dusashewar gani wato Glaucoma, a Najeriya, ya nuna cewa mutane da dama na da cutar ba tare da sanin suna da ita ba. Binciken dai ya nuna cewa kashi biyar cikin dari na masu shekara 40 zuwa sama, a kasar na da cutar. Cutar ta Glaucoma dai tana […]

Masu kitso za su fara gano tabon cin zarafi a kan mata

Masu kitso za su fara gano tabon cin zarafi a kan mata

Ana horas da masu gyaran gashi don gano alamun da ke nuna ko abokan zaman waɗanda suke yi wa kitso sun musguna musu. Wata mai gidan gyaran gashi Beau salon a yankin Norwich cikin Burtaniya ce ta bijiro da wannan tunani, bayan ta gano wata doka da ake ƙoƙarin ɓullo da ita a Amurka wadda […]

‘Na yi ɓarin ciki sau biyar saboda magagin baccin mijina’

‘Na yi ɓarin ciki sau biyar saboda magagin baccin mijina’

Lindsey Roberts wacce bazawara ce a yanzu, ta ce sau biyar tana barin ciki saboda dukan da mijinta Andrew yake yi mata a lokacin da yake cikin magagin bacci a yayin da a yanzu ta gurfanar da hukumar tsaron kasar a gaban kotu. Ta shaida wa BBC cewa “ban san mijin nawa yana da magagin […]

Wata mai ciwon ajali tana nema wa mijinta matar aure

Wata mai ciwon ajali tana nema wa mijinta matar aure

Wata marubuciya da ta gamu da sankarar mahaifa kuma likitoci suka ce ta ajali ce, ta rubuta taƙaitaccen kundin halayen mijinta ta yadda zai samu “wata mai ƙaunarsa”. Amy Krouse Rosenthal ta zayyana nagartattun halayen mai gidanta Jason kuma ta ce tana fatan “wadda ta dace za ta karanta kuma ta samu…”. Ta rubuta a […]

Bincike ya gano alaka tsakanin kiba da cutar kansa

Bincike ya gano alaka tsakanin kiba da cutar kansa

Masu bincike a Birtaniya sun gano cewa akwai dangantaka mai karfi tsakanin kiba da kuma cutar sankara ko cancer a Turance. Masu binciken kimiyyar na cibiyar Imperial College da ke birnin Landan sun ce, mutanen da suke da kiba sosai sun fi sirara hadarin kamuwa da samfurin cutar Kansa iri 11 da suka hada da, […]

Addu’a Ga Shugaba Buhari Shi Yafi Mahimmanci

Addu’a Ga Shugaba Buhari Shi Yafi Mahimmanci

WASHINGTON, DC — Majalisar yaran Najeriya, sun gudanar da addu’oi, na masamman domin neman Allah ya baiwa shugaban najeriya, Muhammadu Buhari, sauki sama da wata guda Kenan dai shugaban yake kasar Ingila inda ake duba lafiyarsa. Mr. Patrick Ikemi, shugaban majalisar yaran Najeriya da akasarinsu ‘yan kasa da shekaru goma sha hudu ne zuwa kasa, […]

‘Yawan cin kayan marmari na iya kawo tsawon rai’

‘Yawan cin kayan marmari na iya kawo tsawon rai’

Masu bincike sun bayyana cewa yawan cin kayan marmari da ganyayyaki a ko wacce rana na iya sa tsawon rai. A wani binciken da kwalejin Imperial ta Biritaniya ta gudanar, ya nuna cewa irin wannan kayan abinci za su iya kare mutane milliyan 7.8 daga mutuwa sanadin kananan cututtuka a ko wace shekara. The team […]

India: Dan siyasa ya bai wa wurin bauta kudin gwamnati

India: Dan siyasa ya bai wa wurin bauta kudin gwamnati

An soki lamirin wani dan siyasar kasar Indiya, bayan da ya kashe dala 750 na kudin gwamnati wajen sayen gwala-gwalan da ya bayar sadaka ga wani wurin bauta. Chandrashekkhar Rao ya bayar da sadakar ne ga wani fitaccen wajen bautar addinin Hindu mai suna Tirumala, saboda nuna farin ciki da kirkiro wata sabuwar jiha mai […]

Kiran AU ta kare ‘yan Nigeria shirme ne — Afirka ta Kudu

Kiran AU ta kare ‘yan Nigeria shirme ne — Afirka ta Kudu

Gwamnatin Afirka ta Kudu ta yi fatali da kiran da Najeriya ta yi ga kungiyar Tarayyar Afirka da ta kare ‘ya’yanta mazauna can. Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Afirka ta Kudu ta kuma yi fatali da ikirarin Najeriya cewa an kai wa ‘yan kasar harin kyamar baki. Mai magana da yawun ma’aikatar Clayson Monyela, ya […]

Kenya ta kafa dokar yaki da fari

Kenya ta kafa dokar yaki da fari

A nahiyar Afirka, kekashewar yanayi na daya daga cikin abubuwan da ke addabar al’umma. Shekara da shekaru da suka gabata, kasashen nahiyar da dama na gudanar da tsare-tsare, kan ta yadda za su shawo kan wannan matsala da ke hana ruwa guda ta fanin cigaba. Gwamnatin kasar Kenya ta bayar da sanarwar kafa dokar ta-bace […]

An sa dokar hana mata bulaguro ba muharrami a Libya

An sa dokar hana mata bulaguro ba muharrami a Libya

Shugaban rundunar sojin kasar Abdul Razzaq Al-Naduri, ne ya sanya wannan dokar. Umarnin ya hada da haramta musu hawa jirgi don tafiya wata kasa su kadai ba tare da muharrami ba a filin jirgin saman Labraq da ke Kudancin kasar. A karshen makon da ya gabata ne dokar ta fara aiki kuma ta jawo cece-kuce […]

Muryar Amurka Na Ziyarar Kulla Dangantaka Da Sauran Kafofin Yada Labarai

Muryar Amurka Na Ziyarar Kulla Dangantaka Da Sauran Kafofin Yada Labarai

WASHINGTON, DC — A ziyarar da babban editan sasahen Hausa na Muryar Amurka, Alhaji Aliyu Mustapha, ke yi yanzu haka a Arewacin Najeriya ya yada zango a jihar Borno. Inda ya ziyarci wasu kafofin yada labarai don kokarin kulla zumunta. Da farko ya fara ziyarar ne da gidan radiyon da ake kiransa Peace FM dake […]

Cinikin makamai ya karu a duniya

Cinikin makamai ya karu a duniya

Wani sabon rahoto da a gudanar, ya bayyana cewa ba a taba samun wani lokaci da aka yi cinikin makamai a duniya kamar dan tsakanin nan ba tun bayan yakin Duniya na biyu. Kwararru a cibiyar Stockholm Internation Peace Research da suka fitar da sakamakon binciken, sun ce yawan makaman da aka yi cinikinsu tsakanin […]

Nigeria: An ɓullo da na’urar magance satar shanu

Nigeria: An ɓullo da na’urar magance satar shanu

A Nigeria, matsalar satar shanu matsala ce da ta daɗe tana ciwa al’umma da hukumomi tuwo a ƙwarya. Duk da cewa Nigeria na cikin ƙungiyar ƙasashe masu tabbatar da lafiyar dabbobi na duniya, rashin samar da hanyoyin tantance dabbobi a shekarun baya ya kasance wani babban ƙalubale ga ƙasar. Wannan yasa wasu ƙwararru suka ɓullo […]