Shugaba Buhari ‘zai ci gaba da huta wa’

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce zai ci gaba da hutwa bayan ya koma gida daga jinyar makwanni bakwai da ya yi a Birtaniya.

Da yake magana ga manyan jami’an gwamnatinsa a Abuja, ya ce mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ne zai ci gaba da jan ragamar al’amura.

Da sanyin safiyar ranar Juma’a ne ya sauka a filin jirgin saman soji da ke birnin Kaduna daga London.

Har yanzu babu cikakken bayani kan abin da ke damun shugaban amma jami’ansa sun nace cewa babu wani abin damuwa a cikin lamarin.

Shugaba Buhari ya ce “Yana samun sauki sosai” amma ya kara da cewar yana bukatar ayi masa wasu karin gwaje-gwaje.

Shugaban ya isake cincirindon ‘yan fadarsa wadanda suka tarbe shi lokacin da ya isa Abuja.

Wakilin BBC Haruna Tangaza ya ce ya ga ministocin shugaban da wasu gwamnoni da dama, “Dukkansu suna cikin walwala da farin ciki.”

 

Source: BBC Hausa