Home » Posts tagged with » Donald Trump

An ayyana dukiyar da manyan jami’an gwamnatin Trump suka mallaka

An ayyana dukiyar da manyan jami’an gwamnatin Trump suka mallaka

Wasu takardu da fadar gwamnatin Amurka ta fitar sun nuna makudan kudin da manyan jami’an gwamnatin Donald Trump suka mallaka. Takardun sun nuna cewa ‘yar gidan shugaban kasar Ivanka da mijinta, Jared Kushner, suna da kaddarorin da suka kai tsakanin $240m da $740m. Hakan ya hada da jarin da suke da shi a Otal-otal din […]

Ba mu damu da barazanar Trump ba — OPEC

Ba mu damu da barazanar Trump ba — OPEC

A baya-bayan nan, wasu manyan kasashe da ke kan gaba ta fuskar sayen man fetur irin su Amurka da China sun bayyana aniyar sauya hanyoyin da suke samun makamashi ga masana’antunsu. Ga misali Amurka ta ce za ta dogara kan man da za ta rika haka a cikin gida da kuma wanda tuni ta saya […]

Gwamnatin Obama ta yi mani sata – Trump

Gwamnatin Obama ta yi mani sata – Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya zargi gwamnatin Obama da ta shude da satar bayanan wayarsa a ofishinsa na Hasumiyar Trump dake birnin New York, a lokacin yakin neman zaben da ya gabata. A wani jerin sakwannin Tweeter, Mista Trump, bai bayar da wata shaida ko hujja ba game da zargin, amma ya bayyana satar bayanan […]

Fitaccen Jarumi Arnold ya ajiye aiki saboda Trump

Fitaccen Jarumi Arnold ya ajiye aiki saboda Trump

Arnold Schwarzenegger ya ajiye aikin gabatar da wani shirin talbiji mai suna The New Celebrity Apprentice, saboda a cewarsa shugaba Donald Trump ya ɓata shi. A wata hira da kafar yaɗa labarai ta Empire, jarumin kuma tsohon gwamnan California ya yi iƙirarin cewa ƙarancin masu kallon shirin na da alaƙa da sunan shugaba Trump a […]

Babban lauyan Amurka ya tsame hannu a bincike kan Rasha

Babban lauyan Amurka ya tsame hannu a bincike kan Rasha

Babban lauyan Amurka, Jeff Sessions ya tsame hannunsa daga binciken da hukumar FBI ke gudanarwa game da zargin katsalandan ɗin Rasha a zaɓen ƙasar. ‘Yan jam’iyyar adawa ta Dimokrat sun buƙaci ya sauka daga kan muƙaminsa lokacin da ta bayyana cewa ya gana da jakadan Rasha yayin yaƙin neman zaɓen shugaban Amurka. Babban lauyan gwamnatin […]

Trump ya dora wa Obama alhakin zanga-zangar kin ‘yan jam’iyyar Republikan

Trump ya dora wa Obama alhakin zanga-zangar kin ‘yan jam’iyyar Republikan

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce ya yi amannar cewar Barack Obama ne ya kitsa jerin zanga-zangar kin ‘yan majalisar dokokin kasar na jam’iyyar Republikan da kuma fitar da wasu bayanan tsaron kasar. Trump ya shaida gidan talabijin na Fox News cewar, “ina tunanin shugaba Obama ne ya kitsa lamarin saboda tabbas mutanensa ne suka […]

Trump ya yi wa majalisa jawabi a karon farko

Trump ya yi wa majalisa jawabi a karon farko

A jawabi na farko da ya yiwa ‘yan majalisar dokokin Amurka tun bayan shan rantsuwar kama aiki a watan da ya wuce, shugaba Trump ya yi alkawarin yin garanbawul ga manufofin kasar. Ya ce lokaci ya yi da ya kamata Amurkawa su tabbatar da mafarkinsu, zai bukaci majalisa ta sanya hannu dan fitar da dala […]

Trump ba zai halarci liyafar ‘yan jarida ta bana ba

Trump ba zai halarci liyafar ‘yan jarida ta bana ba

Shugaba Donald trump ya ce ba zai halarci liyafar cin abincin dare tare da ‘yan jarida da aka saba yi ba duk shekara a fadar White House a wani mataki na kara tsamama dangantaka tsakanin shi da su. Ko a ranar juma’a da ta gabata, an hana gidajen jarida irin BBC, da CNN da New […]

An hana wasu kafafen watsa labarai shiga taron Trump

An hana wasu kafafen watsa labarai shiga taron Trump

Fadar White House ta hana wasu manyan kafafen watsa labarai shiga wurin wani taro da Shugaba Trump ya yi. An hana BBC da CNN da the New York Times da kuma wasu manyan kafafen watsa labarai daga shiga wurin jawabin da kakakin fadar ta White House Sean Spicer ya hada ba tare da gaya musu […]

Trump ya soke kariyar da ake bai wa masu sauya jinsi

Trump ya soke kariyar da ake bai wa masu sauya jinsi

Gwamnatin Donald Trump ta soke kariyar da Amurka ke bai wa daliban da suka sauya jinsinsu na ainihi. Wannan kariya dai na bai wa daliban damar yin amfani da ban dakunan makaranta daidai da jinsin da suka zaba. Ma’aikatar shari’ah da ta ilmi a Amurka sun ce tsare-tsaren da aka bijiro da su bara a […]

Ɗan Mexicon da ‘Trump’ ya kora daga Amurka ya kashe kansa

Ɗan Mexicon da ‘Trump’ ya kora daga Amurka ya kashe kansa

Wani dan kasar Mexico ya kashe kansa sa’a daya bayan an fitar da shi daga Amurka. Guadalupe Olivas Valencia, mai shekara 45, ya fado daga kan wata gada da ke kusa da kan iyakar kasashen biyu bayan an fitar da shi daga Amurka a karo na uku. An same shi a cikin halin rai-kwakwai-mutu-kwakwai a […]

Trump ya fitar da sabbin ƙa’idojin korar baƙin-haure

Trump ya fitar da sabbin ƙa’idojin korar baƙin-haure

Gwamnatin Donald Trump ta fitar da wasu sababbin tsauraran ƙa’idoji wadanda za su sanya a hanzarta korar baƙin-haure daga Amurka. Ka’idodjin za su tabbatar cewa an kori mutanen da ba su da takardun izinin zama a kasar idan sun karya dokokin hanya ko kuma suka yi sata a kantuna kamar yadda ake yi wa wadanda […]

‘Yan siyasa irin Donald Trump sun raba kan duniya – Amnesty

‘Yan siyasa irin Donald Trump sun raba kan duniya – Amnesty

Amnesty International ta ce ‘yan siyasar da ke yin amfani da kalaman raba kawuna suna jefa duniya cikin mummunan hatsari. A rahotonta na shekara-shekara, Amnesty ta ce mutane irin su Shugaba Donald Trump na cikin misalan ‘yan siyasar da suka sanya ake mayar da fagen siyasa tamkar “na kyama da raba kan jama’a”. Rahoton ya […]

Ina goyon bayan manufar Trump — Mugabe

Ina goyon bayan manufar Trump — Mugabe

Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe, ya ce yana goyon bayan shugaba Donald Trump kan manufarsa ta kare muradun Amurka da Amurkawa. A jawabinsa na farko kan kamun ludayin mulkin Mista Trump, shugaba Mugabe ya ce ya yi mamaki kwarai da ya lashe zaben, duk da cewa dama ba ya goyon bayan ‘yar takarar jam’iyyar Democrat […]

Kimiyya: Za a gudanar da zanga-zanga a Amurka

Kimiyya: Za a gudanar da zanga-zanga a Amurka

Shugaban kungiyar masu bincike mafi girma a duniya, ya nuna goyon bayansa kan wata zanga-zanga da aka shirya yi a birnin Washington saboda matakin da shugaba Trump ya dauka na nuna rashin amincewa da binciken kimiyya. Shugaban kungiyar Rush Holt ya bayyana goyon bayan shi ga gangamin da za a yi a watan Afrilun shekarar […]

‘Yan jarida ba sa fadin gaskiya — Trump

‘Yan jarida ba sa fadin gaskiya — Trump

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sake kalubalantar gidajen jaridar kasar, in da ya bayana su da marasa ‘fadin gaskiya’ kuma masu ‘son cimma burinsu’, a lokacin wani gangamin magoya baya, a jihar Florida. Mista Trump ya shaida wa taron cewa ‘Yan jarida ‘ba su so fadin gaskiya ba’ kan zabensa sannan suna da ‘ajendar da […]

Shin Nigeria za ta iya sayen makamai daga Amurka?

Shin Nigeria za ta iya sayen makamai daga Amurka?

Da sabuwar gwamnatin Amurka, Najeriya na da damar ta kara kaimi wajen yakin da take yi da kungiyar ‘yan Boko Haram. Yakin da sojojin Najeriya ke yi da kungiyar Boko Haram ya samu nakasu sakamakon wasu takunkumi da Amurkar ta saka wa kasar a baya. Amurka ta aike wa Najeriya da masu bai wa sojoji […]