Home » Posts tagged with » Facebook

Kamfanin Twitter ya rufe shafukan ‘yan ta’adda 377,000

Kamfanin Twitter ya rufe shafukan ‘yan ta’adda 377,000

Kamfanin Twitter ya ce ya rufe shafukan mutane akalla 636,248 daga tsakiyar shekarar 2015. Kamfanin ya kara da cewa ya kulle kusan shafuka 377,000 na mutanen da ke rura wutar ta’addanci a karshen shekarar da ta gabata An samu kari a kan shafukan da suka rufe na ‘yan ta’adda gabanin wannan lokaci, ko da yake […]

Pakistan na son Facebook ta taimaka wajen yakar batanci

Pakistan na son Facebook ta taimaka wajen yakar batanci

Kasar Pakistan ta nemi shafin sada zumunta na Facebook ya taimaka wajen binciken yada ababen batanci. Kasar Pakistan ta ce ta bukaci shafin sada zumuntan ya taimaka wajen binciko “kalaman batanci” wadanda ‘yan kasar Pakistan ke yadawa a shafukan na Facebook. A cewar Ministan cikin gidan kasar, Chaudhry Nisar, ya ce kasart Pakistan za ta […]

Shin ya kamata a sanya ido kan shafukan sada zumunta?

Shin ya kamata a sanya ido kan shafukan sada zumunta?

Batun sanya ido kan yadda ake amfani da shafukan sada zumunta na zamani a Najeriya al’amari ne da ke saurin tayar da jijiyoyin wuya, saboda yadda aka samu sabanin fahimta a kansa. ‘Yan kasar da dama na ganin sanya ido kan shafukan na sada zumunta wani yunkuri ne na danne hakkin da kundin tsarin mulki […]

Zuckerberg ya ce ana kafar-ungulu ga tsarin dunkulewar duniya

Zuckerberg ya ce ana kafar-ungulu ga tsarin dunkulewar duniya

A wata hira da ya yi da BBC, Mr Zuckerberg ya ce labaran kanzon-kurege da ra’ayoyi masu raba kawunan jama’a da kuma irin bayanan da ake aikawa mutum ta shafukan zumunta bisa bayanan mu’amalarsa a intanet suna yin illa ga jama’a. Ya kara da cewa bunkasar harkokin duniya ta sa an bar mutane a baya, […]

An ci Facebook tarar dala miliyan 500 a Amurka

Masu taimaka wa alkali yanke hukunci sun samu kamfanin Oculus, wanda Facebook ya saya a shekarar 2014, da laifin saba yarjejeniyar kwantiragin da ya kulla da kamfanin Zenimax. An kulla yarjejeniyar ce a lokacin da yake kaddamar da na’urarsa ta saurare da kallon wasannin video wadda ake sakalawa a ka. Kamfanin Oculus ya ce bai […]