Home » Posts tagged with » South Africa

South Africa: Matsin lamba na karuwa kan Shugaba Jacob Zuma

South Africa: Matsin lamba na karuwa kan Shugaba Jacob Zuma

Babbar kungiyar kwadago ta Afirka ta Kudu mai karfin fada aji ta Cosatu, ta bukaci Shugaba Jacob Zuma ya sauka daga kan mulki. Sakatare Janar na kungiyar Bheki Ntshalintshali ya ce a yanzu, “ba shi ne” ya dace ya mulki kasar ba. Mista Zuma ya dade yana fuskantar matsin lamba bayan ya yi wasu muhimman […]

Allah Ya yi wa Ahmed Kathrada na Afirka ta Kudu rasuwa

Allah Ya yi wa Ahmed Kathrada na Afirka ta Kudu rasuwa

Allah Ya yi wa fitaccen dan siyasar Afirka ta Kudun nan Ahmed Kathrada, rasuwa yana da shekara 87. Cibiyar Mista Kathrada, wacce ke kula da al’amuransa, ta ce ya mutu ne a asibitin Donald Gordon a birnin Johannesburg bayan wata gajeriyar rashin lafiya. Shi dai makusanci ne ga marigayi tsohon Shugaban Afirka ta Kudu Nelson […]

Nigeria za ta yi zaman a yi ta ta ƙare da Afirka ta Kudu

Nigeria za ta yi zaman a yi ta ta ƙare da Afirka ta Kudu

Wani ayarin majalisar wakilan Najeriya na musamman yana kan hanyar zuwa Afirka ta Kudu ranar Litinin don bin kadin `yan kasar waɗanda hare-haren nuna ƙyamar baƙi suka ritsa da su a baya-bayan nan. Ayarin dai na fatan tattaunawa da takwarorinsu ‘yan majalisar Afirka ta Kudu domin lalubo hanyar magance wannan matsala. A makwannin baya ne […]

‘Yan Afirka ta Kudu da ‘yan ci rani sun yi fito-na-fito

‘Yan Afirka ta Kudu da ‘yan ci rani sun yi fito-na-fito

‘Yan sanda a Afirka ta Kudu sun yi ta harba hayaki mai sa hawaye da harsashin roba domin tarwatsa daruruwan ‘yan kasar da baki ‘yan ci rani, wadanda ke maci a Pretoria babban birnin kasar, sakamakon wawushe shagunan ‘yan ci rani da aka yi a farkon makon nan. ‘Yan kasar da baki ‘yan ci ranin […]

Najeriya Za Ta Bi Kadun ‘Yan Kasar Da Rikicin Afirka Ta Kudu Ya Shafa

Najeriya Za Ta Bi Kadun ‘Yan Kasar Da Rikicin Afirka Ta Kudu Ya Shafa

Gwamnatin Najeriya ta ce za ta bi kadun `yan kasar da aka jikkata tare da kona musu dukiya a kasar Afirka ta kudu, biyo bayan rikicin kyamar baki. WASHINGTON, DC — Gwamnatin Najeriya ta ce ta samu cikakken bayani akan abin da ya faru a rahotan da jami’an jakadancinta suka aika mata. Rahotan ya nuna […]

Matasa sun kai harin ramuwar-gayya kan ofishin MTN

Matasa sun kai harin ramuwar-gayya kan ofishin MTN

Wasu masu zanga-zanga a Najeriya sun kai wa ofishin kamfanin wayar sadarwa na MTN hari a Abuja, babban birnin kasar. Masu zanga-zangar sun kai hari ne don nuna fushinsu a kan hare-haren kin jinin baki da aka kai wa baki da suka hada da ‘yan Najeriya a Afirka ta Kudu. Duk da cewa ba su […]

Kiran AU ta kare ‘yan Nigeria shirme ne — Afirka ta Kudu

Kiran AU ta kare ‘yan Nigeria shirme ne — Afirka ta Kudu

Gwamnatin Afirka ta Kudu ta yi fatali da kiran da Najeriya ta yi ga kungiyar Tarayyar Afirka da ta kare ‘ya’yanta mazauna can. Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Afirka ta Kudu ta kuma yi fatali da ikirarin Najeriya cewa an kai wa ‘yan kasar harin kyamar baki. Mai magana da yawun ma’aikatar Clayson Monyela, ya […]

An wawushe shagunan baki a Afirka ta Kudu

An wawushe shagunan baki a Afirka ta Kudu

Wata Jaridar Afirka ta Kudu ta ambato mai magana da yawun ‘yan sanda, Bongi Msimango, yana cewa an wawushe kayayyakin shagunan kusan 30 na bakaken fata ‘yan wasu kasashen da ke zama a Afirka Ta Kudu, a ranar Litinin da daddare, a Pretoria, babban birnin kasar. Mista Msimango ya ce, “An fasa shagunan bakin ne […]