Trump ya fitar da sabbin ƙa’idojin korar baƙin-haure

Gwamnatin Donald Trump ta fitar da wasu sababbin tsauraran ƙa’idoji wadanda za su sanya a hanzarta korar baƙin-haure daga Amurka.

Ka’idodjin za su tabbatar cewa an kori mutanen da ba su da takardun izinin zama a kasar idan sun karya dokokin hanya ko kuma suka yi sata a kantuna kamar yadda ake yi wa wadanda aka kama da aikata manyan laifuka.

Ka’idojin ba su yi karan-tsaye ga dokokin shige-da-fice na kasar ba, sai dai za su tsananta kan aiwatar da hukunce-hukunce.

An yi kiyasin cewa akwai baƙin-haure miliyan 11 a Amurka.

A ranar Talata, kakakin fadar White House Sean Spicer ya ce sababbin ka’idojin ba za su sanya a fitar da baƙin-haure da dama lokaci guda ba, yana mai cewa an tsara su ne domin su karfafa wa jami’an tsaro tabbatar da dokokin da ake amfani da su.

A cewarsa,”Sakon da fadar White House da kuma ma’aikatar tsaron cikin gida ke son aikewa shi ne mutanen da ke zaune a kasar na, wadanda ke yi mata barazana, su za su fara ficewa daga cikinta.”

Wasudaga cikin sabbin ƙa’idojin:

  • Fadada shirin korar mutanen da ba su da takardun izinin zama, wadanda aka kama da aikata laifuka
  • Kawo karshen dokar kasar ta sakin mutanen da aka kama a kan iyakokin kasar maimakon wuraren da ake tsare su har sai an kammala batunsu.
  • Kira ga mahukunta su tuhumi iyayen da suka taimaka wajen shigar da ‘ya’yansu kasar
  • Amincewa a aiwatar da shirye-shiryen fadada gina katanga a kan iyakokar Amurka daga bangaren kudu
Source: BBC Hausa