Ya ya Nigeria za ta yi da N5.2trn na asusun TSA?

'Yan Najeriya na ta faman neman sanin hakikanin abin da za a yi da makudan kudaden da gwamnatin tarayya ta tara, ta hanyar asusun bai-daya na TSA.

A ranar Talata ne dai Babban Akantan Kasar, Ahmed Idris, ya bayyana wa ‘yan jarida cewa yanzu haka akwai tsabar kudi har Naira Tiriliyan biyar da biliyan 244.

“Daga 10 ga watan Fabrairun 2017, kudade da yawansu ya kai Naira Tiriliyan 5.244 sun shiga aljihun Babban Bankin Najeriya. Mun kuma samu damar rufe asusun ajiyar kudi har guda dubu 20.” in ji Idris.

An dai ce wadannan asusun da aka rufe mallakar ma’aikatun gwamnatin kasar ne da suke amfani da su a bankuna daban-daban.

Dangane kuma da yadda za a yi da kudaden, Mista Idris, ya ce, kudaden suna hannun babban bankin kasar wato CBN, kafin daga bisani gwamnati kuma ta san abin da za ta yi da su.

Kudaden dai da aka tara a asusun na TSA wato Naira Tiriliyan 5.224, sun fi kasafin kudin shekara, lokacin tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan.

Sannan kuma tazarar kudaden da kasafin kudi na 2016 wanda gwamnatin shugaba Buhari ta fara yi, ba yawa.

Wasu dai na ganin cewa ya kamata a yi amfani da wadannan makudan kudaden wajen cike gibin kasafin kudin 2017, maimakon ciwo wa kasar bashi domin cike gibin.

Kasafin kudin 2017 dai ya kama Naira Tiriliyan bakwai da biliyan 298.

Daga cikin kasafin, za a ciyo bashin Naira Tiriliyan biyu da biliyan 32, daga kasashen waje da kuma cikin gida.

Wannan ne ya sanya wasu ke ganin za a iya amfani da Naira Tiriliyan 5.244 da aka tara a Asusun Bai-daya, maimakon a ciyo wa kasar bashi.

Sai dai kuma wasu masana na cewa gwamnatin tarayya ba ta da ikon yin amfani da kudaden ba tare da amincewar Majalisar Dokokin kasar ba.

A watan Agustan 2015 ne dai shugaba Buhari, ya bayar da umarni yin amfani da Asusun na Bai-daya wajen biya ko kuma karbar kudade daga hannun ma’aikatun gwamnatin tarayya.

Hakan dai ya biyo bayan irin yadda gwamnatin Buhari ta ce, gwamnatin tsohon shugaban kasar, Goodluck Jonathan ta wawashe asusun kasar.

Da kuma aniyar gwamnatin Buhari ta yaki da rashawa da cin hanci da aka ce ta nan ne arzikin kasar yake zurarewa.

Source: BBC Hausa