‘Yadda muka kama masu ‘safarar jarirai’ a Jos’

Ibrahim Idris ya lashi takobin yaki da manyan laifuka

Hukumomin tsaro a jihar Filato da ke Nijeriya, sun ce, sun kama wasu wasu mutane da suka hada maza da mata,da ake zargi da safarar jarirai.

An dai kama mutanen ne a Jos, babban birnin jihar, cikinsu har da wata mai ciki da ke gab da haihuwa.

Hukumomi sun ce mutanen da aka kama dai sun hada da ‘yan mata da akan yi wa ciki su haihu domin sayar da jariran da kuma wasu maza da ake zargi da ajiye ‘yan matan suna yi musu ciki.

Manjo Janar Nicolas Rogers, shi ne kwamandan Rundunar Tsaro ta Musamman da ke aikin kiyaye zaman lafiya a jihar ta Filato.

Ga kuma karin bayanin da ya yi kan kamun da suka yi, a hirarsa da Ishaq Khalid.

Source: BBC Hausa