Yadda rikicin Kudancin Kaduna ke tsorata masu zuba jari

Tashe-tashen hankulan da suke faruwa a tsakanin mazauna yankin Kudancin Jihar Kaduna da suke kawo barazana ga tsaro tare da haifar da kashe-kashen mutanen da ake zargin ’yan bindiga na aikatawa a wasu kananan hukumomi a yankin na matukar jawo koma-baya ga harkokin kasuwanci da tattalin arzikin yankin.
Rikici na baya-bayan nan ya samo asali ne a shekarar 2011 lokacin rikicin bayan zaben Shugaban kasa, inda a lokacin wasu kabilun yankin suka fada wa Fulani makiyaya da sauran Hausawan yankin don daukar fansar zargin da suke yi na kashe mutanensu a cikin garin Kaduna.
A lokacin an rika kashe Fulani makiyaya da ke wucewa ta yankin a kan hanyarsu ta komawa garuruwansu, inda matasan Kudancin Kadunan suka far wa Fulanin suka hallaka da yawa daga cikinsu tare da kashe musu shanu masu yawa.
Wannan ne ya sa ake zargin Fulanin da sha alwashin daukar fansa a kan jama’ar yankin kuma tun daga wancan lokaci ake ta asarar rayuka da dukiyoyi a yankin har ta kai ga kabilun yankin ga zargin Fulanin da suke zaune tare da su a yankunan da hannu a kashe-kashen zargin da shugabannin Fulanin suka dade suna karyatawa.
Wasu majiyoyi masu tushe sun ce an rika yi wa juna dauki-daidai a tsakanin makiyaya da manoma a yankin, inda Fulani makiyaya a yankin suke kukan ana kashe musu ’ya’ya a duk lokacin da suka fita kiwo, yayin da manoma suke kukan cewa Fulanin suna kawo musu hare-hare suna kashe su.
Rikicin wanda yake tashi ya kwanta, a tsakiyar shekarar da ta gabata, ya sake kunno kai a dajin garin Ninte da ke kusa da Gada-Biyu a gundumar Godogodo da ke karamar Hukumar Jama’a.
Daga Ninte ne rikicin na Kudancin Kaduna ya karaso kulkofa da ke tsakanin Gada-Biyu da Godogodo inda aka zargi kabilun garin da kai farmaki ga wani Bafulatani da ke zaune a garin tsawom shekaru. Daga nan sai ya fada Gada-Biyu ya karasa Godogodo, inda aka kone tare da rushe babban Masallacin Juma’ar garin da kuma kone Masalllacin Juma’a na Izala.
A can gefe kuma matasa ’yan asalin yankin musamman a kan hanyar Kafanchan zuwa Kagoro zuwa kaura da kaura zuwa Zangon Kataf, sai matasan kabilu suka shiga tare tituna suna zabar Hausawa ko Fulani da ke tafiya a cikin motoci suna kashewa. Wannan zargi ya fito fili ne a cikin wata sanarwa da kungiyar Jama’atu Nasril Islam reshen Jihar Kaduna ta raba wa manema labarai a Kaduna. “Muna kira ga gwamnatin jihar ta kawo karshen tsare hanya da kuma rikicin da ke faruwa a Kudancin jihar,” inji Sakataren Jama’atu na Jihar, Ibrahim Kufena a cikin sanarwar.
Wannan ya sa ’yan kasuwa da ke zuwa cin kasuwanni a kananan hukumomin Jema’a da kaura da Zangon-Kataf inda rikicin ya fi kamari suka kaurace wa yankin domin tsira da rayukansu ta hanyar kauce wa kisan dauki-daidai da matasa ke yi musu a kan hanya.
Aminiya ta samu rahotannin da ke cewa a cikin watan Nuwamban bara akalla ’yan kasuwa 14 aka hallaka a Samarun Kataf lokacin da suke hanyarsu ta zuwa Kaduna daga Jihar Filato.
Lokacin da Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i ya ziyarci garin Kafanchan don ganin abin da zanga-zangar lumana da ta rikide rikici ta haifar tare da kwantar da kurar da ta taso ne matasan yankin suka kai masa farmaki suna jifar ayarin motocinsa bayan ya tsaya domin ya saurari koke-koken wadansu mata da suka fitozanga-zanga tsirara don nuna rashin jin dadinsu kan kashe-kashen da suke faruwa a yankin.
Wannan rikici yana shafar tattalin arzikin yankin domin hatta kamfanonin kasashen waje da suka bayyana niyyarsu ta zuba jari a yankin musamman a Kamfanin Citta na Kachiya (Kachia Genger Processing Company) da ke Kachiya suka janye daga yarjejeniyar da suka kulla da gwamnatin jihar na farfado da kamfanin, inda suka ce idan har za a kai hari ga Gwamnan, babu tabbacin za su samu kariya daga hare-haren da jama’ar yankin za su iya kai musu.
Haka akwai wani kamfani daga kasar Austireliya da shi ma ya janye shirinsa na zuba jarin wajen hako ma’adanin da aka gano watannin baya a garin Dangoma da ke karamar Hukumar Jema’a.
Shi kansa Gwamna El-Rufa’i ya tabbatar da kauracewar masu zuba jarin bayan kwana biyu da jefarsa sa a yankin, inda ya ce duk bayanin da ya yi wa masu zuba jarin don su hakura su ci gaba da harkokinsu sun ki yarda. “Wannan babbar matsala ce kuma asara ce ga yankin domin kamfanin da suka nemi zuba jari kan noma da sarrafa citta a Kamfanin Citta na Kachiya sun ce ba za su iya ba. Har ila yau kamfanin kasar Austireliya da ya nuna sha’awar zuba jari a garin Dangoma mai arzikin ma’adinai a Jama’a ya ce zai janye saboda rashin tsaro a yankin. Sai dai duk da haka a matsayina na Gwamna ina kokarin shawo kansu domin na san amfaninsu a yankin. Wannan shi ne matsalar rashin tsaro,” inji Gwamnan.
Bayanin ya tayar wa masu kishin ci gaban jihar hankali saboda janyenwar manyan kamfanonin ba asara ce kadai ga yankin Kudancin Jihar ba, har da da daukacin jihar. Kuma daruruwan matasan yankin da za a dauka aiki su ma sun yi asara. Rikicin da kuma matsalar satar mutane sun taka rawa wajen nuna kin amincewa da maido da sauka da tashin jirgin sama daga Abuja zuwa Kaduna a sakamakon rufe filin jirgin saman Abuja da Gwamnatin Tarayya ke son yi a watan Maris don yi masa gyare-gyare.
Rahotanni sun ce shugabannin wasu manyan kamfanonin jiregen sama na kasashen waje sun nuna damuwarsu game da canja akalar saukar jiregensu zuwa Kaduna inda suke nuna cewa akwai rashin tsaro a jihar.
Wannan ya sa masana tattalin arziki ke nuna damuwa, inda suka bukaci gwamnati ta yi mai yiwuwa wajen wayar wa jama’a kai ta hanyar nuna masu cewa mafi yawan labaran da suke karantawa kan rashin tsaro a Kudancin Jihar bai shafi sauran yankunan jihar ba kuma ko a Kudancin akwai kananan hukumomi da abin bai shafe su ba.
Masanan sun ce yin hakan zai taimaka wajen cire tsoro a zukatan baki masu niyyar zuba jari a fannoni daban-daban a fadin jahar.
Shugaban Majalisar Malamai da Limamai ta Jihar Sheikh Abubakar Baban Tune ya roki gwamnatin jihar ta kawo karshen rikici tare da hukunta duk wanda ke da hannu wajen hura wutar rikicin.
Tuni dai aka tura bataliya biyu ta sojoji zuwa yankin inda suke sintiri domin kawo karshen kisan da ake aikatawa.
Kuma a ranar Talatar da ta gabata Gwamna El-Rufa’i ya yi albishir din cewa an kama wadansu daga cikin masu kisa hare-hare da kashe-kashen da ake yi a Kudancin Kaduna.
Gwamna El-Rufa’i ya bayyana wadanda ake zargi lokacin da ya ziyarci Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, Mista Agyle Abeh. Ya sha alwashin cewa gwamnati za ta tabbatar da an zakulo dukkan wadanda suke da hannu a hare-haren tare da hukunta su.
Sai ya bukaci al’ummar jihar su rungumi zaman lafiya da hakuri da juna domin tabbatar da ci gaban jihar.
Tunda farko sai da Kwamishinan ’Yan sanda ya gabatar da wadansu daga cikin wadanda ake zargi ga Gwamnan, inda ya ce an kama su ne kan laifuffuka da dama da suka hada da tayar da rikici a Kudancin Kaduna da fashi da makami da satar mutane. Ya ba Gwamnan tabbaci cewa rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba, har sai ta raba jihar da miyagu.

Source: Aminiya