‘Yan Iran za su yi aikin Hajjin bana — Saudiyya

Kasar Saudiyya ta ce ‘yan kasar Iran za su halacci aikin Hajjin bana, bayan da suka rasa damar halartar na bara sakamakon tsamin da dangantaka ta yi tsakanin gwamnatin Iran din da masarautar Saudiyya.

Dangantaka dai ta yi tsami matuka tsakanin manyan kasashen biyu masu karfin fada a ji a yankin Gabas ta tsakiya, bayan da ‘Alhazai fiye da 1000 suka rasu a Mina’ a wani turmutsutsu da ya faru a lokacin aikin Hajjin 2015.

Batun bayar da bisa da batun tsaro sune suka zama manyan dalilan rashin zuwan nasu.

Amma masarautar Saudiyya ta ce an cimma yarjejeniya bayan tattaunawa tsakanin kasashen biyu.

Aikin Hajji na daga cikin manyan shika-shikan Musulunci guda biyar, kuma ana so ko wanne Musulmi ya yi idan har ya samu ikon zuwa.

Shekarar da ta gabata ta zamo lokaci na farko da ‘yan kasar Iran ba su samu damar halartar aikin Hajji ba, cikin kusan shekaru 30 da suka gabata.

Har yanzu dai ba a san ainihin adadin wadanda suka rasa ransu a iftila’in ba. Saudiyya ta ce mutum 769 ne, yayin da lissafin da kasashen duniya daban-daban suka yi na mutanensu da suka mutu ya bayar da adadin cewa mutum 2,426 ne suka mutu.

Iran ta ce ‘yan kasarta 464 ne suka mutu, kuma biyan diyya ga iyalan wadanda suka mutun shi ne babban jigon sasantawa wajen yardar Iran ta halarci aikin Hajjin banan.

Duk da rahoton cewa an cimma yarjejeniya, har yanzu ana ‘yar nuna yatsa tsakanin kasashen biyu, inda Saudiyya ke zargin Iran da rura wutar rikici inda ‘take goyon bayan mayakan Shi’a a yankin.’

Iran dai ta yi watsi da zargin, ta kuma ce dole Saudiyya ‘ta dakatar da goyon bayan kungiyoyin ‘yan tawaye na Sunni da take yi.’

Source: BBC Hausa