‘Yan Nigeria sun hana jirgi tashi a Birtaniya

An kama mutum 17 bayan wata zanga-zanga da suka yi a filin jirgin saman Stansted da ke garin Essex, wadda ta dakatar da tashi da saukar jiragen sama na wucin gadi a ranar Talata.

Da misalin karfe 9:30 na dare aka kira ‘yan sanda bayan da wata kungiyar wasu mutane ta shige filin jiragen sama kuma suka kulle kansu cikin wani sama.

Wadanda ke da hannu a lamarin na kokarin dakatar da wani jirgin sama ne, wanda suka yi ikrarin cewa zai kwashi wasu ‘yan Najeriya da ‘yan Ghana ya mayar da su kasashensu.

Wani mai magana da yawun filin jirgin saman ya ce an rufe titin da jiragen saman ke bi ne a matsayin wani matakin tsaro, amma kuma sai aka sake bude shi da misalin karfe 11.17 na dare.

Karin bayani

An karkatar da jirage 23 da suka yi niyyar sauka a filin jirgin saman zuwa wasu filayen jiragen sama wadanda suka da, wadanda suka taho daga Naples da Cologne da Glasgow da Riga da Belfast da kuma Bilbao.

Mai magana da yawun filin jirgin sama ya ce zanga-zangar ta faru ne a wasu kauyuka da ke kusa da filin jirgin saman da kamfanoni masu zaman kansu ke amfani da shi, wanda yake da taraza daga sauran titunan da jiragen ke amfani da su.

An shawo kan matsalar cikin gaggawa

A ranar Laraba ne ‘yan sandan Essex suka ce jami’ai sun je wurin da lamarin ya faru kuma sun yi kokarin fitar da masu zanga-zanga daga cikin jirgin, wanda a da zai tafi Najeriy.

Wani babban jami’in dan sanda, Sean O’Callaghan ya ce, ‘yan sanda sun shawo kan masu zanga-zangar da ke wani bangare na filin jirgin cikin gaggawa.

Ya kara da cewa, “Za mu ci gaba da aikin tare da abokan huldarmu da hukumomin filin jirgin saman domin mu hukunta wadanda suka aikata laifin ba tare da an bata lokaci ba.

Masu fafutuka sun wallafa hotunan zanga-zangar a shafukan sada zumunta da muhawara, har ma da hotunan mutane da ke kwance a kasa, kuma jami’an tsaro na zagaye da su.

A wani abu da suka wallafa a shafin Facebook, sun ce za a tursasawa ‘yan Najeriya da ‘yan Ghana da dama su koma kasashensu, amma kuma ba a tabbatar da hakan ba.

Daya daga cikin masu zanga-zangar, Susan James, ta ce “Ba zan iya yin shuru a daidai lokacin da ake kokarin mayar da wasu a asirce kuma cikin gaggaw ba.”

Source: BBC Hausa